Kungiya Ta Karrama Matawalle, Ta Fadi Nasarorin da Ya Samu a Minista
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya samu yabo daga wajen wata ƙungiya kan ƙoƙarin da yake yi
- Ƙungiyar ICNGO ta karrama ministan a matsayin wanda babu kamarsa a watan Nuwamba saboda samar da tsaro a Arewacin Najeriya
- Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa ƙoƙarin ƙaramin ministan ya jawo an samu nasarori wajen magance ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar International Defence Group Organisation (ICNGO) ta karrama ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ƙungiyar ICNGO ta bayyana Bello Matawalle a matsayin ministan da babu kamarsa a watan Nuwamba, saboda nasarorin da ya samu wajen magance rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ICNGO, Frank Augustine ya fitar a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ICNGO ta karrama Bello Matawalle?
Ƙungiyar ta bayyana irin matakan da Matawalle ya ɗauka, waɗanda suka ƙara inganta tsaro a Sokoto, Zamfara, da sauran jihohin Arewa, rahoton Tribune ya tabbatar.
"Muhimman nasarorin da aka samu sun haɗa da dawo da tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma rage yawan cin zarafin mata musamman a yankin Sokoto."
"A cikin ƙanƙanin lokaci, ƙoƙarin da Matawalle ya yi ya haifar da kwanciyar hankali a Arewacin Najeriya, tare da samun nasarorin da suka cancanci yabo a duk faɗin ƙasar nan."
- Frank Augustine
Waɗanne nasarori Matawalle ya samu?
Ƙungiyar ta nuna cewa tun lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya tura shi jihar Sokoto a watan Satumban 2023, Matawalle ya jagoranci ayyukan soji da dama, inda aka kashe sama da ƴan bindiga 6,000 tare da kawar da manyan ƴan ta’adda.
Daga cikin manyan shugabannin ƴan ta'addan da aka kashe akwai, Alhaji Halilu Sububu da masu biyayya ga Dan-Isuhu da Dogo Sule a jihar Zamfara.
Matawalle ya kai ƴan jarida kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya maka wasu fitattun yan jaridu a Arewacin kasar nan a gaban kotu.
Bello Matawalle ya ɗauki matakin ne bisa zargin yan jaridun da wallafa labaran karya da cin zarafinsa a kan matsalar tsaron ƙasar nan.
Asali: Legit.ng