Kannywood: Rahama Sadau da Jarumai Mata 11 da Suka Yi Aure daga 2022 zuwa 2025
Kano - Kannywood ta kasance ɗaya daga cikin masana’antu mafiya tasiri wajen yada al’adu da nishaɗantar da al’ummar Hausawa a nahiyar Afrika.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amma abin da ya fi daukar hankali ba fina-finai kawai ba ne, har da rayuwar jaruman a zahiri. Masu kallo da masoya suna yawan bibiyar duk wani abu da ya shafi jarumai: daga tufafin da suke sanyawa, gidajen da suke rayuwa, zuwa auratayyarsu.

Asali: Instagram
A tsakanin shekarun 2022 zuwa 2025, jarumai mata 12 ne suka yi aure, inda a shekarar 2022 kadai aka daura auren jarumai bakwai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta tattaro cikakken bayani game da jarumai 10 da suka yi aure a tsakanin 2022 zuwa 2025, inda za a ga sunayen jarumai, ranakun aure, mazajen da suka aura, da garuruwan da aka yi bikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2022: Shekarar auratayya a Kannywood
Shekarar 2022 ta shiga tarihi a masana'antar Kannywood, domin a shekarar ne jarumai mata masu yawa suka yi aure.
1. Aisha Aliyu Tsamiya

Asali: Instagram
A ranar 25 ga Fabrairun 2022, fitacciyar jarumar Kannywood, A'isha Aliyu Tsamiya ta ba masoyanta mamaki, inda aka ji aurenta kwatsam.
Duk da cewar A'isha Tsamiya tana cikin ganiyar shahararta a lokacin, haka aka yi auren a sirrance, babu wanda ya ga katin gayyata balle wani taro.
A'isha Tsamiya ta boye bayanai game da wanda za ta aura, wanda ya kara fito da irin kallon da ake yi mata na daya daga cikin matan Kannywood masu kamun kai.
Har yanzu tsohuwar Jarumar Kannywood, A'isha Aliyu Tsamiya tana tare da mijinta, wanda daga bisani aka gano sunansa Alhaji Buba Abubakar.
2. Hafsat Idris (Barauniya)

Asali: Instagram
Kamar dai yadda A'isha Tsamiya ta yi, ita ma mawakiya Hafsat Idris wacce aka fi sani da Hafsat Barauniya ta yi aurenta a sirrance a ranar 26 ga Fabrairun 2022.

Kara karanta wannan
Al Makura: Ƴan bindiga sun bi dare, sun sace hadimin tsohon gwamna, an bazama daji
Wannan auren sirri da Hafsat Barauniya ta yi ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin ta ƙi sanar da auren ne don boye bayanan wanda za ta aura.
A wannan gabar ne ma aka fara yaɗa jita-jitar cewa Hafsat Barauniya ta auri wani ɗan ahalin Abacha ne, jita-jitar da jarumar ta zo ta zo ta ƙaryata daga baya.
A lokacin ne Hafsat Barauniya ta tabbatar wa duniya cewa ta yi auren, amma dai ta ki bayyana wanda ta aura.
Amma a watan Yulin 2025, Legit Hausa ta ruwaito cewa auren Hafsat Barauniya da na jaruma Zahra'u Shata ya mutu.
3. Hassana Muhammad

Asali: Instagram
Hassana Muhammad na daya daga cikin Jaruman Kannywood da suka yi aure a lokacin da suke ganiyar shahararsu.
A ranar 13 ga Maris ne aka daura auren jarumar da babban mai shirya fina-finai, Abubakar Bashir Maishadda, wanda ya samu halartar ƴan masana'antar.
Jarumi Ya'u Shareef ya shaida wa Legit Hausa cewa fim din Hauwa Kulu na kamfanin Maishadda Global Resources ne Hassana ta yi na karshe.
An daura auren Bashir Maishadda da Hassana Muhammad a masallacin Juma'a na Murtala da ke jihar Kano kamar yadda muka ruwaito.
4. Ummi Rahab

Asali: Facebook
A ranar 13 ga Yunin 2022, aka daura auren fitacciyar matashiyar ƴar wasar Hausa, Ummi Rahab da angonta Abdulrahman Muhammad (Lilin Baba).
Wannan aure da aka yi tsakanin jaruma Ummi Rahab da Lilin Baba, wanda shi ma jarumi ne amma ya fi shahara a fagen waka, ya ja hankali sosai.
Masoyan Ummi Rahab sun kasance tare da ita ne tun tana ƴar ƙaramarta har ta girma a masana'antar, wanda ya sa auren nata ya shahara.
Ana ganin wannan auren nasu ya kara nuna yadda jaruman fim din Hausa ke son auren junansu, kuma an tabbatar da cewa ma'auratan sun samu ƙaruwa.
5. Amina Lawan (Raliya Dadin Kowa)
An daura auren jarumar shirin Dadin Kowa, Amina Lawan, wacce aka fi sani da Raliya a karshen watan Yulin 2022 a masallacin Juma'a na Old BUK da ke Kano.
Jaruma Raliya ta yi aure ne yayin da tauraruwarta ke haskawa a masana'antar fim, musamman saboda karbuwar da shirin Dadin Kowa ya yi.
Jaridar Aminiya ta ce auren Raliya ya samu halartar manyan abokan aikinta, la'akari da cewa mahaifiyarta ta dade a hakar fina-finan Hausa, inda take fitowa a cikin shirin na Dadinkowa a matsayin Sabuwa, matar Ayuba Maigadi.
6. Rukayya Dawayya

Asali: Instagram
Fitacciyar jarumar Kannywood da aka dade ana damawa da ita a masana'antar, Rukayya Dawayya ta shiga daga ciki a shekarar 2022.
An rahoto cewa an daura auren Jaruma Rukayya Dawayya da Sama'ila Na'abba Afakallah (Shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta Kano a wancan lokaci) a masallacin Tinshama da ke Kano.
Wannan aure na Dawayya da Afakallah ya ja hankalin mutane sosai la'akari da shuhurar jarumar da kuma matsayin mijin a masana'antar nishadi ta Kano.
Har yanzu Rukayayya Dawayya na tare da Mijinta Isma'ila Afakallah, kuma Allah ya albarka ce su da samun zuriya.
7. Halima Yusuf Atete

Asali: Facebook
A karshen Nuwambar 2022 ne aka daura auren 'yar wasan fim, Halima Yusuf Atete tare da wani dan kasuwa, Alhaji Muhammad Kalla a Maiduguri.
Halima Atete ta samu goma sha tara ta arziki daga 'yan wasan Kannywood, ma'aikata da kuma masoyanta, domin an sha shagali a bikinta.
Ko daga hotunan da Atete da Alhaji Kalla suka sauka, wanda jaridar Blueprint ta wallafa za ka gasgata irin soyayyar da ke tsakanin mutanen biyu.
Abokan sana'ar Halima Atete, ciki har da Ali Nuhu, Ahmad Bifa, da mai shirya fina-finai Abubakar Mai Shadda, sun bayyana farin cikinsu a gare ta.
2023: Shekarar auren jaruma Rashida
8. Rashida Mai Sa'a

Asali: Instagram
Ba a samu yawan auratayya a masana'antar Kannywood a shekarar 2023 ba idan aka kwantanta da shekarar 2022.
Duk da shirun da aka samu a shagulgulan biki a 2023, jaruma Rashida Adamu Abdullahi, ta angwance da masoyinta, Alhaji Aliyu Adamu a cikin shekarar.
Mun ruwaito cewa Rashida Mai Sa'a kamar yadda ake kiran jarumar ta auri Alhaji Aliyu, Sardaunan Matasan Gwoza a ranar 11 ga Nuwambar 2023.
An daura auren ne a Unguwar Mallam Bello da ke Daurawa, jihar Kano, kuma ya samu halartar masoya, jarumai da ma'aikatan masana'antar Kannywood.
2024: Aure da zawarcin Mansura
9. Mansura Isah
A cikin watan Yunin 2024 ne muka samu labarin cewa tsohuwar matar jarumi kuma mawaki, Sani Musa Danja, watau Mansura ta yi aure.
Aminiyar jarumar, Samira Ahmed ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Instagram a daren ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
Tsohuwar jaruma Mansura Isa na ci gaba da shirya fina-finan Hausa da sauran ayyukan jin-kai da take yi.
2025: Fitattun jarumai sun shiga daga ciki
A cikin shekarar 2025, an ga wasu fitattun jaruman Kannywood mata sun yi aure, inda auren uku daga cikinsu ya fi yin fice.
10. Aisha Humaira

Asali: Facebook
A ranar 25 ga watan Afrilun 2025 muka ruwaito cewa fitacciyar 'yar wasan Hausa, Aisha Humaira ta shiga daga ciki.
An rahoto cewa an daura auren Aisha Humaira da ubangidanta, mawaki Dauda Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara a masallacin Juma'a na Maiduguri.
Fitattun mutane a Najeriya da aka ce sun halarci bikin sun hada da Sanata Barau Jibrin (mataimakin shugaban majalisar dattawa) da kuma tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari.
Wannan aure dai ya ja hankalin mutane sosai a kafafen sada zumunta, domin an nade ana zargin Aisha da Rarara suna soyayya la'akari da irin shakuwar da suka yi.
Auren Aisha Humaira da Dauda Kahutu Rarara shi ne aure mafi girma da aka yi a 2025, domin ya hada babbar jaruma da fitaccen mawaki.
11. Maryam Malika

Asali: Facebook
Aure na biyu a 2025 da ya ja hankalin mutane a Kannywood shi ne auren jaruma Maryam Malika da jarumi Abdul M. Shareef, kamar yadda muka ruwaito.
An daura auren Maryam da Abdul a ranar 27 ga Yunin 2025 a masallacin Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, jihar Kaduna, wanda wakilin Legit Hausa ya halarta.
An gudanar da shagulgula kafin ranar daurin auren, kamar taron cin abincin dare, buga kwallon angon da amarya, taron kawaye da sauransu.
Maryam Malika da Abdul M Shareef sun shafe shakera suna soyayya da juna, har dai daga karshe Allah ya tabbatar da aurensu.
12. Rahama Sadau

Asali: Instagram
Auren fitaccen jaruma kuma mai shirya fina-finai, Rahama Sadau ya zo wa mutane a ba-zata, domin har zuwa ranar daurin auren duniya ba ta san da labarin ba.
Har sai da aka je wajen daurin auren ne aka fara fitar da hotuna da bayanai game da auren, domin Sadau da kannanta sun yi amfani da dabara wajen sirranta auren.
Legit Hausa ta rahoto cewa an daura auren Rahama Sadau da mijinta Ibrahim Garba a Kaduna, kuma an yi auren ne kamar a cikin sirri don ba a ga tarin mutane ba.
Duk da wannan ba-zata da jarumar ta yi, masoyanta sun nuna farin ciki tare da yabonta kan irin wannan mataki da ta dauka na yin aure yayin da take ganiyar shahararta.
Auren 'yan Kannywood na jawo ce-ce-ku-ce
A wani labarin, mun ruwaito cewa, auren jaruman Kannywood na yawan tayar ƙura a kusan kowane lokaci, tun daga shagalin biki, da tarukan murna da aka shirya.
Kannywood ba ta tsira daga sharrin jita-jita da kage ba domin a wasu lokutan tun kafin a ɗaura aure, mutane ke fara bincike don gano aibun jaruman matuƙar aka san suna soyayya
Hakazalika, a duk lokacin da ƴan Kannywood za su yi aure, mutane na zuba ido su ga wane irin biki za a shirya na kece raini da irin kuɗin da za a kashe wanda ke jawo maganganu.
Asali: Legit.ng