Jaruma Rukayya Dawayya zata amarce, ta fitar da hoton angon

Jaruma Rukayya Dawayya zata amarce, ta fitar da hoton angon

  • Fitacciyar jarumar masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rukayya Dawayya, ta kara cin karo da soyayya baya wasu shekaru
  • Jarumar da ta shahara, ta wallafa hoton shugaban MOPPAN, Afakallahu tare da kwarara masa addu'o'i irin na masoya masu cike da shauki
  • Tuni jama'a suka harbo jirginta inda aka gano soyayya ce, babu bata lokaci aka dinga kwarara musu addu'a tare da fatan a kulla alheri

Fitacciyar tsohuwar jarumar masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, za ta amarce.

Legit.ng ta gano hakan ne bayan jarumar ta wallafa hoton masoyinta wanda kuma shine ake fatan ya zama angon, a shafinta na Instagram.

Rukayya Dawayya
Jaruma Rukayya Dawayya zata amarce, ta fitar da hoton angon. Hoto daga @dawattarukayya85
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan gwamnan Zamfara da zuka-zukan 'ya'yansa mata 14 reras

Wanda ta wallafa hoton sa tare da kwarara masa addu'ar masoyan, shine shugaban hukumar tace fina-finai, wato Afakallahu.

Babu jimawa da wallafar masoyanta suka dinga yi mata fatan alheri inda ta dinga amsa addu'o'in da aka yi mata.

Ga abinda wallafar ke cewa mai dauke da hoton Afakallahu:

"Samun masoyi na gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya yayi yawa sai karfin addu'ah. Alhmdulillahi yah rabbi lakal hamdu wash shukhur ALLAH nagode maka daka amsa addu'atah khairun nass man Yan Fa un nass"

A baya dai jarumar tayi shuhura a masana'antar kafin daga bisani tayi aure inda ta haifa yaro namiji mai suna Arfat. Cikin hukuncin Ubangiji, sai Allah ha kawo karshen auren inda jarumar aka ga ta dawo masana'antar duk da tana kasuwancinta a gefe.

Muna musu fatan alheri, tare da fatan Allah yasa abokin arzikin ta ne.

Jama'a sun yi martani

Ga martanin da Legit.ng ta tattaro muku a karkashin wallafar:

Kara karanta wannan

Wankan sallah: Hadadden hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza

@aliscomaimuna yace: "Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya, yasa gidan zama ne."
@bilkisu860 cewa tayi: "Allah ya tabbatar muku da mafificin alkhairi, ina taya ku murna."
@zahrau577: "Allah ya tabbatar da alkhairinsa a gareku yasa abokin arzikinki ne."

Da kanta jarumar ta dinga bin su tana amsa musu da Amin tare da yin godiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel