Mutuwar Auren Hafsat Idris Da Na Zahra’u Shata Ya Gigita Yan Kannywood

Mutuwar Auren Hafsat Idris Da Na Zahra’u Shata Ya Gigita Yan Kannywood

  • An rahoto cewa auren manyan tsoffin jaruman Kannywood, Hafsat Idris Barauniya da Zahra'u Shata sun mutu
  • Labarin mutuwar auren jaruman masana'antar shirya fina-finan ya kada hantar cikin abokan sana'arsu
  • Suna ganin wannan zai kara tabbatar da zargin da ake yi wa matan masana'antar na cewar basa zaman gidan miji

Wasu daga cikin jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sun nuna damuwarsu matuka a kan mutuwar auren wasu tsoffin jarumai mata wato Hafsat Idris wacce aka fi sani da Hafsat Barauniya da kuma Zahra'u Shata.

A cewar jaruman, mutuwar auren nasu zai kara sanya mutane su yarda da zargin da ake yi wa yan fim na cewar basa zaman gidan aure, mujallar fim ta rahoto.

Auren Hafsat da Zahra'u ya mutu
Mutuwar Auren Hafsat Idris Da Na Zahra’u Shata Ya Gigita Yan Kannywood Hoto: Hafsat Idris - Photos/Kannywood a yau
Asali: Facebook

Sun bayyana damuwar tasu ne a yayin zantawa da Mujallar Fim din domin jin ta bakinsu dangane da mutuwar auren manyan taurarin wadanda suka tarkata suka bar gidan mazajen nasu.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Yan Sanda Sun Yi Ram Da Matasa 6 Kan Fashi Da Makami a Bauchi

Kamar yadda rahotanni suka nuna, auren tsoffin jaruman masana'antar ya mutu ne tun watanni da dama da suka shige.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masana abubuwan da ke gudana a masana'antar sun ce sun dade suna tantama a kan matsayin auren Hafsat da Zahra'u musamman duba ga yadda suka koma suna mu'amala da mutane sabanin yadda suke yi a lokacin da suke amsa sunan matan auren.

Tsoffin jaruman sun kara azama wajen daura sakonni a shafukansu na soshiyal midiya musamman ma a kafar Instagram da TikTok, sannan sun koma harkoki sosai a Kannywood.

Menene ya kashe auren Zahra'u Shata?

Zahra’u Shata ta kasance tauraruwar fim a shekarun 2000, inda daga bisani ta yi aure na kece raini da wani shararren dan kasuwa mai suna Alhaji Marwan a Kano a shekarar 2004.

Ta shafe tsawon shekaru 19 a gidan aurenta lamarin da yasa kowa ke mata murna cewa ta banbanta da sauran jarumai da basa zaman aure.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Yan Kannywood Gaba Daya

Wata majiya mai tushe ta sanar da Mujallar Fim cewa auren Zahra'u ya mutu tun a watan Janairun 2023.

Bayan mutuwar auren nata, sai ta zauna a gidan mijinta har zuwa lokacin da ta kammala iddarta inda daga bisani ta kama gidan haya tare da 'ya'yanta a Tudun Yola da ke jihar Kano.

Wata kawar jarumar ta bayyana cewa lallai ta taka muhimmiyar rawar gani wajen kashe aurenta wanda ke da albarkar 'ya'ya har hudu.

A cewar majiyar, tsohuwar jarumar ta biyewa kawaye wadanda suke rayuwar kece raini ta yadda suke samun kudi, manyan gidaje da motoci inda take ganin aurenta ya hana ta fantamawa kamar su don haka ta ga gwanda ta fita.

Wata tsohuwar jarumar masana'antar da ke gidan mijinta wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce a ranar da ta riski labarin mutuwar auren abokiyar aikin tata sai da bacci ya kauracewa idanunta.

Tace:

“Ni wallahi lokacin da aka ce auren Zahra’u ya mutu da kyar na iya barci a daren, kawai na kwanta ina ta juye-juye.”

Kara karanta wannan

Arewa Na Digan Jini Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Mata 23 Da Ma'aikatan Kamfani 10 a Zamfara

Yaushe auren Hafsat Idris ya mutu?

Jaruma Hafsat Idris ta shiga masana'antar Kannywood da kafar dama cikin yan shekaru da suka gabata.

Sai dai kuma kwatsam aka ji jarumar wacce aka fi sani da Hafsat Barauniya ta auri wani matashi mai suna Mukhtar Hassan Hadi, a ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022 cikin sirri a Kano.

An rahoto cewa wata makusanciyar jarumar ta ce sam labarin mutuwar auren bai bata mamaki ba domin dai an gina shi ne a kan turbar sha'awa da biyan bukata daga dukka bangarorin biyu. Auren ya kuma mutu ne tun watanni bakwai da suka gabata.

Majiyar ta ce:

“Hafsat ta auri yaro karami da ta girma nesa ba kusa ba, kuma iyayen sa ba su son auren tun da farko. Sun so ya auri sa’ar sa kuma wacce ba ‘yar fim ba.”

Sai dai kuma an tattaro cewa jarumar na so a mayar da auren amma shi angon bai ba da hadin kai ba.

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

Tuni dai Hafsat ta koma harkar fim inda a yanzu take cikin jaruman shirin fim mai dogon zango wato 'Manyan Mata'.

"Muna bayansa dari bisa dari": Ali Nuhu ya goyi bayan soke lasisin yan Kannywood gaba daya

A wani labarin kuma, mun ji cewa shahararren jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarki ya goyi bayan soke lasisin yan masana'antar da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Ali Nuhu ya jadadda cewar suna tare da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Abba Al-Mustapha, dari bisa dari a kan wannan mataki da suka dauka na soke lasisin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel