Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana

Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana

  • Dubban al'umma sun shaida aure tsakanin Furodusan Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jaruma Hassana Muhammad
  • An daura auren ne a yau Lahadi, 13 ga watan Maris, a Masallacin Murtala da ke Kano
  • Wannan aure ya dauki hankali sosai kasancewar yan masana'antar basu cika auren junansu ba

Kano - A yau Lahadi, 13 ga watan Maris ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin babban furodusan masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jarumar fim, Hassana Mohammed.

Auren wanda aka daura a Masallacin Murtala da ke birnin Kano, ya samu halartan manyan jaruman masana’antar wadanda suka nuna kara sosai ga abokan sana’ar tasu.

Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana
Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana Hoto: realalinuhu/@realabmaishadda
Asali: Instagram

Tun farko dai labarin auren ya ja hankalin jama'a duba ga yadda ba'a cika aure tsakanin yan fim ba, domin sun fi auren yan waje, illa yan tsiraru da suka kulla auratayya a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Bayan daurin auren, Maishadda ya je shafinsa na Instagram domin nuna godiya ga Allah, inda ya yi hamdallah tare da neman masoya da su taya su da addu’a.

Ya rubuta a shafin nasa:

“ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH
“An Daura Aurena Da HASSANA MUHAMMAD. Ina bukatar addu’arku Masoya.”

Jama'a sun yi masu fatan alkhairi

Tuni abokan sana'arsu da sauran mutane suka cika sashin da aka tanada domin sharhi, inda suka yi masu fatan alkhairi.

washafati ta yi martani:

"Allah ya bada zaman lfy "

ayshatulhumairah ta yi masu addu'a:

"Allah Ubangiji ya sanya Alkhairi Yasa Mutuwa ce zata raba ku
"Congrats @realabmaishadda @real_hassana_muhd."

realaeshatsamiyya ta ce:

"Allah ya Baku zaman lfy❤️"

abbaelmustapha1 ya ce:

"Allah ya sanya Alheri Ya Baku zaman Lafiya, Kwanciyar Hankali Da Zuri'a Dayyiba."

Kara karanta wannan

Yayin da yake Kasar Ingila, Buhari ya nada mukami, ya zabi sabon Shugaban HYPREP

ammnur_kayanmata ta ce:

"Allah tabbatar da alkhairi ya bada zaman lafiya."

madam__korede ta ce:

"Allah yasanya Alheri zakuyi Albarka."

Sabbin bidiyoyin Maishadda da Hassana suna rungumar juna kafin aure sun janyo cece-kuce

A baya mun kawo cewa, wasu bidiyoyi da ake ta yadawa na Furodusa Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa Hassana inda aka gansu suna rungumar juna yayin daukar hotunan kafin biki sun janyo cece-kuce.

Wasu daga cikin masoyansu sun dinga yaba musu yayin da wasu kuwa suka dinga tofin Allah wadai da Allah ya shirya kan lamarin ganin cewa ba daura auren aka yi ba.

Wasu sun danganta hakan da yanayin rayuwar 'yan fim da kuma wata irin sabuwar rayuwar wayewa da ta samu jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel