Kannywood: Mawaki Lilin Baba zai yi wuf da jaruma Ummi Rahab, Katin Ɗaura Aure ya bayyana

Kannywood: Mawaki Lilin Baba zai yi wuf da jaruma Ummi Rahab, Katin Ɗaura Aure ya bayyana

  • Ta tabbbata Jarumi kuma mawaƙi Lilin Baba zai shiga daga ciki tare da sahibarsa jaruma Ummi Rahab ta Kannywood
  • Wani Katin gayyatar ɗaura aure da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna za'a ɗaura auren matasan jaruman a watan Yuni, 2022
  • A baya dai alamu sun nuna cewa soyayya da shaƙuwa na ƙara ƙarfi tsakanin Jaruman, Allah ya yi zasu auri juna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jarumi kuma fitaccen mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Shu'aibu Ahmed Idris, zai angonce da masoyiyarsa jaruma Ummi Rahab.

Shafin Kannywoodempire ya saka Katin ɗaura auren jaruman biyu a dandalin Instagram, kuma ya nuna za'a ɗaura auren fitattun jaruman a cikin watan Yuni da muke ciki.

Shuaibu Ahmed Idris wanda aka fi sani da Lilin Baba zai Angonce da sahibarsa Rahab Saleh Ahmed, wato Ummi Rahab a ranar 18 ga watan Yuni 2022.

Kara karanta wannan

Gaskiyar bayani kan wanda Atiku Abubakar ya zaɓa ya zama matamakinsa a zaɓen 2023

Lilin Baba zai Auri Ummhi Rahab.
Kannywood: Mawaki Lilin Baba zai yi wuf da jaruma Ummi Rahab, Katin Ɗaura Aure ya bayyana Hoto: @kannywoodempire
Asali: Instagram

Za'a ɗaura auren Jaruman ne a Tudun Murtala, NEPA office, hannun riga da gidan Bala Kasa, Anguwar Tudun Murtala a Kano da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayyanar katin ɗaura auren matasan jaruman ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan auren su.

Soyayya ta yi karfi tsakanin Jaruman

A watannin da suka shuɗe ne alamu suka nuna soyayya ta yi ƙarfi tsakanin jaruman biyu masu tasowa, inda aka ga Lilin Baba ya yi wasu kalamai ga Ummi Rahab a ranar ƙara shekararta.

A ranar 2 ga watan Fabaraoru, 2022, Ummi Rahab ta yi biki zagayowar ranar haihuwarta, inda ya yin taya ta murna, Lilin Baba ya ce sun kusa shiga daga ciki.

Wani sashin kalaman soyayya da ya aike wa Rahab a wannan rana, Lilin Baba ya ce:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa abar kaunar rayuwata Ummi Rahab. Hakika ke ta daban ce mai zuciyar zinari."

Kara karanta wannan

2023: Na fi kowa tsammanin lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, Gwamnan Arewa

"Ina aika sakon zagayowar ranar haihuwa ta musamman gare ki yayin da kika kara shekara daya a yau! Ina fatan kin cika da farin ciki da annashuwa a yau. Abun farin ciki ne ganin irin matar da kika zama a yau. #HappyBirthday UMMI.
"Ina miki fatan alkhairi a duniya da lahira, Allah ya ci gaba da sanya albarka a rayuwarki. Karin nasara a gare ki . Na kusa yin Wuff da ke Insha Allah."

A wani labarin kuma Ina bukatar Mijin aure cikin gaggawa, Jaruma a masana'antar Fina-Finai ta cire kunya

Jaruma a masana'antar shirya Fina-Finai, Eucharia Anunobi, ta sanar da duniya halin da take ciki na bukatar mijin aure.

Yayin zantawa da kafar watsa labarai, Jarumar ta ce tana son mijin da zata aura ya gaggauta bayyana kuma ya zama cikakken namiji, kyakkyawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel