Kano: Jaruma Raliya ta shirin dadin kowa za ta yi aure, hotuna da katin biki sun fito

Kano: Jaruma Raliya ta shirin dadin kowa za ta yi aure, hotuna da katin biki sun fito

  • Jaruma Amina Lawan wacce aka fi sani da Raliya a shiri mai dogon zango na dadin Kowa, za ta amarce a gobe Juma'a
  • Jarumar mai tasowa ce ta wallafa katin gayyatar aurenta da masoyinta Habibu a shafinta na TikTok tare da bidiyo mai dauke da hotunansu
  • Za a daura auren a masallacin Juma'a na BUK Old Site dake Kano kuma za a rakashe da liyafa a yau Alhamis a Farm Center

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Labarin da Legit.ng Hausa te tattaro a halin yanzu shine jaruma Amina Lawan wacce aka fi sani da Raliya a shirin Dadin Kowa za ta amarce da angonta mai suna Habibu a ranar Juma'a mai zuwa da izinin Allah.

Mun samo wannan sanarwan ne daga shafinta na TikTok inda ta wallafa katin gayyatar daurin auren wanda za a yi shi a ranar Juma'a, 22 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, Jaruma Fati Washa ta maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi a shirin Labarina

Raliya Dadin Kowa
Jaruma Raliya ta shirin dadin kowa za ta yi aure, hotuna da katin biki sun fito. Hoto daga @raliya_Dadin_Kowa
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a daura auren ne a masallacin Juma'a na BUK Old Site bayan kammala sallar Juma'a ta gobe.

Bayan katin gayyatar bikin da jarumar ta fitar, ta fitar da katin gayyatar liyafar cin abincin dare wacce za a yi a ranar Alhamis da karfe biyar na yammaci a Farm Center dake birnin Kano.

Martanin jama'a

@Aààzara: "Allah sarki razaky yasa alkhairi Allah kade fitina"
@Fareeda Abubakar678: "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi"
@menarl: "Amina, Allah ya sanya alkhairi yasa a dace, ya ba ku zuriya dayyiba"

Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito

A wani labari na daban, Fatima Kashim Shettima, kyakyawar diyar 'dan takarar mataimakin shugaban kasan Najeriya, Kashim Shettima na jihar Borno, ta shirya tsaf domin amarcewa da zukeken angonta mai kyau.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari zai kashe wa 'yan Najeriya N6.72trn a matsayin tallafin man fetur

Fatima da kyakyawan angonta mai suna Sadiq Ibrahim Bunu, zasu zama daya kuma alkawarin masoyan zai cika a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli 2022 a garin Maiduguri dake jihar Borno.

Tuni kyawawan hotunan Fatima da zukeken angonta suka fara yawo yayin da shirye-shiryen kasaitaccen aurensu yayi nisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel