“Ina Cikin Mawuyacin Hali”: Adam a Zango Ya Koka Kan Rashin Samun Farin Ciki a Rayuwa

“Ina Cikin Mawuyacin Hali”: Adam a Zango Ya Koka Kan Rashin Samun Farin Ciki a Rayuwa

  • "Ina cikin mawuyacin hali": Adam A Zango ya magantu kan jarabawar rayuwa da yake samun farin ciki a rayuwa
  • Kamar yadda ya wallafa a a shafinsa na Instagram, Zango ya ce burinsa a yanzu ya samu farin ciki ko da kuwa na mako daya ne
  • Abokan sana'arsa a Kannywood da ma masoyansa sun yi martani kan hain da jarumin yake ciki, inda da yawa ke tausasa zuciyarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jarumi kuma mawaki a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Adam A Zango ya bayyana cewa yana cikin wani mawuyacin hali.

Adam A Zango ya fadi irin mawuyacin halin da yake fuskanta a rayuwa
Jarumin ya ce ba zai iya ci gaba da jure azabar da rayuwarsa take fuskanta ba. Hoto: adam_a_zango
Asali: Instagram

Zango ya sanar da hakan ne a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu 2024.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya fito ya gayawa duniya halin da Adam A. Zango ya samu kansa a ciki

A cikin sanarwar da ta fitar, jarumin ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wai shin idan na daina fim na daina waka na hakura da komai na nishadi za a barni in zauna lafiya?"

Baballe Hayatu ya gargadi Zango

Ga dukkan alamu, akwai wani abu da ke damun fitaccen jarumin a zuciyarsa wanda kuma ya gagara dannewa ya fito soshiyal midiya ya bayyana.

Abokin sana'arsa, Baballe Hayatu, ya yi martani kan wannan sakon da Adam Zango ya wallafa yana mai cewa:

"Haba Adamu, me ya yi zafi haka?. Ina ga ai kamar mun yi wannan maganar, idan har akwai wani abu sai ka kira a waya kawai mu nemi mafita tare.
Kar ka bari zuciyarka ta sa ka aikata wani abu da za ka yi da-na-sani a nan gaba. Komai ya yi zafi maganinsa Allah, shin ina imaninka yake?"

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

"Ina cikin mawuyacin hali" - Zango

Sai dai kalaman mawaki Zango, dan asalin jihar Kaduna, sun nuna damuwarsa ba 'yar karama bace, domin ya ce shi kadai ya san mawuyacin halin da yake fuskanta, kuma ba zai iya jurewa ba.

Zango ya ce:

"Ina cikin mawuyacin hali, kuma ba zan iya ci gaba da jurewa ba.
"Ni burina kawai a yanzu in samu farin ciki ko da kuwa na mako daya ne, amma ba zan ci gaba da boye abin da yake raina ba."

Wannan wallafa ta Adam A Zango, ta jawo cece kuce kama daga mabiyansa har zuwa abokan sana'arsa.

Yayin da wasu ke ganin bai dace ya wallafa halin da yake ciki a soshiyal midiya ba, wasu na ganin tsarin rayuwarsa ne ya jefa sa a ciki.

Arewa Focus ya wallafa bayanin da mawakin ya yi, kalla a kasa:

Ga kadan daga ra'ayoyin jama'a

Kara karanta wannan

Kano: An shiga fargaba yayin da gungun matasa suka hallaka wani almajiri ɗan shekaru 16

ayshatulhumairah:

Komai yayi zafi maganin sa Allah. Dukkan abin da yafi karfin ka ba zai fi karfin ubangijin ka ba. Allah ya kawo maka mafita a yayuwarka, ya yaye maka dukkan damuwa"

iam_oga_abdul_:

"Wanda ubangiji keso yafi shiga matsala! Allah yana sane da komai! Ka kara hakuri baba"

taheerkargee:

"Rayuwa sai Hakuri yarima komai yayi zafi maganinsa Allah"

adamsycelebrity:

"Kayi hakuri komai yayi zafi maganinsa Allah, kai da kake da mahaifiya ma a raye, ta yi maka addu'a kawai."

ahmad_80_editor:

"Baba kayı Hakuri duk wadda Allah yake so yafi jarabtassa da Abubuwa iriri"

naija_swagss:

"Ku da kanku Ku kuke rokon daukaka, kuma Allah ya baku, dama Allah yace zan jarabce ku ta inda ba kwa tinani"

yousuf_s_marafa:

Dole sai kayi film zaka samu jin dadi? Kake karanta Qur'ani mana ka gani."

Wa ya taimaka aka ba Ali Nuhu mukami?

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa fitaccen mawakin siyasa a Arewa, Dauda Kahutu Rarara ya sanar da cewa shi ne ya yi ruwa ya yi tsaki Tinubu ya ba Ali Nuhu mukami.

A cewar Rarara duk da Bola Tinubu ya nada Ali Nuhu mukamin daraktan hukumar fina-finai ta Najeriya, har yanzu gwamnati ba ta biya shi wahalar da ya yi a yakin zaben 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel