Akwai Dalili: Shekara 1 Na Shugaba Tinubu Ta Fi Shekaru 8 Na Mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Akwai Dalili: Shekara 1 Na Shugaba Tinubu Ta Fi Shekaru 8 Na Mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

  • A baya-bayan nan wani bankin zuba hannun jari na duniya Goldman Sachs ya ayyana Naira a matsayin kudin da ya fi kowanne tabuka abin a zo a gani a duniya
  • Andrew Matheny, masanin tattalin arziki a bankin na Goldman Sachs, ya bayyana cewa dala za ta iya kara yin kasa da N1,200 nan kusa
  • Majiyar Legit.ng ta ruwaito Reno Omokri na bayyana farin cikinsa ganin yadda darajar Naira ke ci gaba da farfadowa

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa "shekara daya da Bola Tinubu ya yi ya kawo ci gaba a Najeriya fiye da shekaru takwas na Muhammadu Buhari".

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Omokri ya ba da wannan kwatance ne bayan wani bankin hannun zuba jari, Goldman Sachs, ya ayyana Naira a matsayin kudin da ya fi tabuka abin kirkir a duniya a watan Afrilu.

Mulkin Tinubu ya fi na Buhari, inji Omokri
Reno Omokti ya ce gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari dadi | Hoto: Reno Omokri, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Omokri, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya soki wadanda ke hasashe da hangen ci gaba da lalacewar Naira, kudin kasar da ta fi kowacce tattalin arziki a Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na saka mu alfahari da kasancewa 'yan Najeriya

Ya ce, idan aka yi la’akari da ci gaban da aka ce an samu a karkashin gwamnati mai ci, Shugaba Tinubu “sannu a hankali na sanya mu ji alfahari da kasancewarmu ‘yan Najeriya”.

Omokri ya bayyana ra'ayinsa ne ta hanyar yada wani rubutu a shanfisa na Twitter a ranar Asabar, 13 ga Afrilun 2024.

Sai dai wannan al'amari bai gamsar da wasu ba, inda suke bayyana martani kan abin da jigon na PDP ya fadi a kasan rubutunsa.

Kara karanta wannan

Naira ta koma gidan jiya, kudin Najeriya ya dawo mafi rashin daraja a duniya

Ga cikakken batun Omokri:

Mulkin Tinubu ya fara da kunci

Idan baku manta ba, 'yan Najeriya sun bayyana shiga kunci tun bayan da shugaban kasa Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a ranar da aka rantsar dashi.

Wannan ya biyo wasu manyan matakai da suka kai ga tashin kayayyaki, ciki har da janye tallafin karatu da na wutar lantarki a Najeriya.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago kan makomar aiki a kasar.

Yadda dala ta sauka a ranar Juma'a

A wani labarin, kun ji yadda a ranar Juma’ar da ta gabata aka ji Naira ta sake kara daraja a kasuwannin canji inda ta kasance a kan N1, 150 idan aka kwatanta da dala.

‘Yan canji da ke kasuwanci a Legas sun saye Dala a kan N1, 110 sannan suka rika saidawa a kan N1, 150 da makon nan ya zo karshe.

A baya, dalar ta doshi Naira 2000, inda gwamnati ta gaggauta daukar matakan tabbatar da an samu hanyoyin ceto darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel