A karon farko Baballe Hayatu yayi magana akan abubuwan da suke haddasa rikici a Kannywood

A karon farko Baballe Hayatu yayi magana akan abubuwan da suke haddasa rikici a Kannywood

- Daya daga cikin jarumai maza na masana’antar Kannywood, Baballe Hayatu ya bayyana babbar matsalar masana’antar

- Jarumin ya ce, yanci da kowa ke da shi ne da kuma rashin girmama na gaba a masana’anatar shi ya hana cece-kuce karewa

- Ya ce matukar za a dinga hakuri, a san ciwon kai, a mutunta juna da kuma gujewa yayata fada a soshiyal midiya, toh masana’antar zata zauna lafiya

Daya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood wanda ya dade yana taka muhimmiyar rawa a masana’antar, ya bayyana cewa rashin sanin ciwon kai da rashin girmama juna, a matsayin abubuwan da suka fi komai ci mai tuwo a kwarya. Yadda kowa yake da yancin yin abinda ya ga dama, ba tare da tunanin wanda yake sama dashi ba.

Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da suke tattaunawa da wakilin Northflix.ng, inda yake tambayarasa me yake ganin yana kawo cece-kucen da baya karewa a masana’antar Kannywood.

Baballe ya bayyana cewa, “Rashin hakuri na rayuwa da kuma rashin daraja juna ne. Duk masana’antar duniya ana samun irin wannan matsalar amma ina ganin namu ya fi yawa. Kuma duk sakamakon rashin sanin mutuncin juna ne.”

Jarumin y ace, “Ita rayuwa zo mu zauna, zo mu saba ce. Sai dai kuma idan kana da matsala da mutum bai kamata a ce ka yayata shi a duniya ba ta yadda kowa sai ya sani ba. Gara ka nemi mutum ku yi yaku-yaku.

KU KARANTA: Ko a jikina zagina da 'yan soshiyal midiya ke yi - Rahama Sadau

"Yawan yada korafe-korafe a soshiyal midiya ba komai bane face tonon asiri. A ganina gara mu yi ta a tsakaninmu ba tare da kowa ya sani ba. Kamar yadda na fada a baya, ita rayuwa zo mu zauna ce kuma zo mu saba. Don haka rashin sanin ciwon kai da rashin mutunta juna da rashin hakuri, su ke jawo mana wannan babbar matsalar.

"Idan har zamu gyara wadannan abubuwa guda biyu, yaro ya girmama babba, babba kuma ya girmama na kasa da shi saboda wanzar da zaman lafiya, toh duk wadannan abubuwan zasu wuce a masana’antar kuma za a samu zaman lafiya da juna.” A cewar Baballe Hayatu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel