Likafa ta cigaba: Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa

Likafa ta cigaba: Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa

Shararen jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam Zango, zai tafi kasar Faransa domin hallartan nadin sarauta da za'ayi wa wasu hausawa mazauna kasar inda kuma ake sa ran zaiyi wasa a wajen taron.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Zango zai yi waka a taron da za ayi a ranar 23 ga watan Yuni na 2018 wanda zai samu hallartan hausa daga ma wasu kasashen turai.

Likafa ta cigaba: Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa
Likafa ta cigaba: Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa

"Ina murnar sanar da ku masoya na cewa an gayyace ni zuwa nadin sarauatan wasu muhimman mutane da hausawa mazauna kasar Faransa za su dauki nauyin gudanarwa.

"Za'a karama mutane da dama daga kasashen Kamaru, Chadi, Jamhuriyar Congo, Ghana da kuma wasu kasashen turai kuma ina daga cikin wanda aka gayyata don inyi waka a wajen taron," inji shi.

KU KARANTA: Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

Masoya jarumin sunyi tururuwa zuwa shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram don taya shi murnar wannan karamci da akayi masa tare da yi masa fatan alkhairi.

Zango yana daya daga cikin jaruman Kannywood da su kayi fice wajen wakokin Hausa wanda hakan yasa wasu ke yi masa lakabi da 'Davido na Arewa' inda suke kwatanta shi da shahararen mawakin Najeriya Davido.

Baya ga haka Zango ya sami nasarori sosai a matsayinsa na jarumin fim da kuma mai shirya fina-finai. Wasu daga cikin fina-finansa da su kayi farin jini sosai sun hada da Basaja da Gwaska.

A shekarar 2016, Zango ya samu rashin jituwa da jaruma Rahama Sadau inda su kayi ta musayar maganganu amma daga baya Sadau ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa tuni sun shirya da Zangon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164