Kannywood: An Gano Babban Kuskure da Aminu Saira Ya Tafka a Shirin Labarina

Kannywood: An Gano Babban Kuskure da Aminu Saira Ya Tafka a Shirin Labarina

  • Wani masanin kiwon lafiya, Ibrahim Musa ya bankado wasu kura-kura da Aminu Saira ya tafka a shirinsa na Labarina
  • Ibrahim Musa ya yi magana ne kan Labarina zango na 9 kashi na 12 a bangaren da aka nuna hukuncin likita kan matsalar Maryam
  • Masanin ya ce kuskure ne ace ita matar ba zata haihu ba don kawai ita da mijinta suna da AS, kuma sikila ba ta jawo barin ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shirin Labarina mai dogon zango daga kamfanin Saira Movies shi ne kusan a kan gaba a cikin shirye-shiryen Kannywood masu dogon zango a wannan lokaci.

Sai dai, kasancewar shirin yana samun miliyoyin masu kallo ya sa masana suka rika bibiyarshi domin yin fashin baki tare da gano inda kura-kurai suke.

Kara karanta wannan

Rigima ta kaure tsakanin fitacciyar jarumar Kannywood da mabiyanta a soshiyal midiya

Masanin kiwon lafiya ya gano kurakurai a shirin Labarin
An ba Aminu Saira kan kurakuran da yake aikatawa a shirin Labarina. Hoto: Labarina Series
Asali: Facebook

Wani masanin kiwon lafiya, da ya yi karatu a jami'ar kiwon lafiya ta Kudancin Carolina (MUSC), Ibrahim Musa ya wallafa wasu kura-kuran da aka tafka a Labarina a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarina zango na 9 kashi na 12

KAmar kowanne kashi na shirin Labarina zango na 9, shi ma kashi na 12 ya zo da nashi sabon salon, wanda ya ja hankalin jama'a tare da kara tamke zaren labarin shirin.

An ga yadda jagoran shirin, Mai Nasara (Sadiq Sani Sadiq) ya shiga bakin ciki sakamakon barewar cikin da Maryam (Fatima Hussaini Abbas) ke dauke da shi.

Mahaifiyar Maryam ta yi kalaman da suka kara tabbatar da dattakonta, na lallai sai dai Maryam da Mai Nasara su rabu ma damar haihuwa za ta zama matsala tsakaninsu.

A hannu daya kuma, ana hasashen matsalar da Maryam ta samu shi zai bude kofa ga likita Asiya (Zarah Diamond) ta samu damar auren shahararren mai kudin.

Kara karanta wannan

Shin da gaske an aikawa malamai N16m domin hana matasa zanga-zanga a Arewa?

Likita ya gano kuskure a shirin Labarina

Masanin kiwon lafiya, Ibrahim Musa ya nuna damuwarsa kan yadda mai ba da umarni na shirin Labarina, Mallam Aminu Saira ke kin tuntubar masana kiwon lafiya a ayyukansa.

Ibrahim Musa ya ce:

"Da farko dai AS da AS idan su ka yi aure matar ta samu ciki, suna da yiwuwar samun zuriya mai cutar sikila 25% (1:4). Kuma ko da jaririn da ke ciki yana da sikila ba zai zama sanadin barin ciki ba.
"Kuskure na farko shine nuna cewa cikin ya bare ne saboda jaririn yana da sikila. Kuskure na biyu shine yarda likitan Labarina ke ba Mainasara shawarwari kan abin da ya shafi rayuwarsa."

Bayanin masani kan cutar sikila a jikin jariri

Bayan zayyano wadannan kurakuren, masanin kiwon lafiyar ya ce:

"Shi sickle cell ba matsala bace ga dan dake cikin uwa saboda a wannan lokacin duk 'hemoglobin' dinsa F.

Kara karanta wannan

Malami ya kasafta yadda karamin ma’aikaci zai karar da albashin N70, 000 a abinci a wata

"Sai bayan an haifi jariri da kamar wata uku zuwa shida 'hemoglobin' F ke canjawa zuwa 'hemoglobin' S. A wannan matakin ne ciwon sikila ke bayyana a zahiri ya yi tasiri."

Ibrahim Musa ya jaddada cewa kuskure ne ace ita matar ba za ta haihu ba don kawai ita da mijinta suna da AS.

Me likita ya kamata ya fadawa Mai Nasara?

Dangane da yadda likitan shirin ke ba Mai Nasara shawarwari, Ibrahim Musa ya ce:

"Shi zaman ba da shawara ana yin sa ne domin ma'aurata su fahimci menene hatsarin kamuwa da ciwo ko yada shi ga zuriyarsu.
"Abu na farko da ake koyawa mai ba da shawara shine kada ya taba saka baki akan zabin da ma'auratan za su yiwa kansu.
Kuma ma'auratan ake hadawa a wuri daya ayi musu bayani gamsasshe sai ace suje suyi shawara a tsakaninsu."

Masanin ya ce kuskure ne a nuna likita ya ware miji shi kadai ya ce masa sai dai su daina haihuwa ko su rabu domin ba aikin sa bane kuma shawara bace ta ilimi.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Sheikh Gumi ya karfafi guiwar matasa, ya soki malamai

Me ke jawo irin wannan matsalar?

A zantawarmu da marubuci Najib Abdulaziz, ya ce akwai marubutan ba sa yin bincike mai zurfi yayin da suke yin rubutu, wasu kuma suna yi dai dai gwargwado.

Najib Abdulaziz ya ce wasu lokutan kuma daraktoci na sauya abin da marubuci ya rubuta, idan bai gane wajen ba ko abin da aka rubuta ba zai samu a wajen daukar shirin ba.

Duk da hakan, Najib ya yi kira ga marubuta da ma daraktoci da su kasance masu zurfafa bincike yayin rubutu da daukar shirin fim domin magance ire-iren wadannan matsaloli.

Nafisa ta yiwa masu zaginta martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ta harzuka da irin yadda wasu mabiyanta ke fada mata bakaken maganganu a intanet.

Bayan sun kaita makura, jarumar ta ware lokaci inda ta rika mayar masu da martani dai dai bakar maganar da suka yi mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.