Ana Tsaka da Jimamin Rasuwar Jaruma Fati Slow, Wani Daraktan Fina Finai Ya Rasu

Ana Tsaka da Jimamin Rasuwar Jaruma Fati Slow, Wani Daraktan Fina Finai Ya Rasu

  • Yayin da ake jimamin rasuwar jarumar Kannywood, Fati Slow, wani jarumin fina-finan Nollywood ya yi bankwana da duniya
  • An sanar da labarin mutuwar marigayin wanda darakta ne kuma marubuci a jiya Litinin 27 ga watan Mayu a birnin Lagos
  • Wannan na zuwa ne yayin da masana'antar ke jimamin yadda ake yawan mutuwa da suka fi mutum 10 daga watan Janairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - An sake shiga jimami a masana'antar shirya fina-finan Nollywood bayan rasuwar fitaccen darakta.

An sanar da mutuwar marigayi Reginald Ibere wanda ya kasance darakta kuma marubuci a jiya Litinin 27 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

An dauki mataki kan 'dan sandan da aka nadi bidiyonsa yana karbar 'na goro' a Imo

Bayan rasuwar Fati Slow, fitaccen daraktan fina-finai ya rasu
An sanar da rasuwar fitaccen daraktan fina-finai, Reginald Ibere ana tsaka da jimamin mutuwar Fati Slow. Hoto: @reginald_ebere.
Asali: Instagram

Jarumin fina-finan Nollywood ya mutu

Shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Segun Arinze shi ya tabbatar da haka ga jaridar TheCable a jiya Litinin 27 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Arinze bai bayyana ranar da fitaccen daraktan ya yi ban-kwana da duniya ba ko kuma cutar da ta yi ajalinsa.

Daga cikin fina-finan marigayin akwai Gateman’ da ‘Wicked Love’ da ‘Living with a Ghost', cewar rahoton Leadership.

Sauran sun hada da Commitment Shy’ da ‘The Devil da the Red Sea’ da ‘Tangled Web’ da ‘The Unwanted’ da ‘Biological Clock’.

Tuni aka fara tura sakon jaje musamman daga masana'antar fina-finan bayan samun labarin mutuwar marigayin tare da nuna alhini kan wannan babban rashi.

Jaruman fina-finan Nollywood da suka mutu

Tun farkon watan Janairun 2024, masana'antar ta rasa jarumai da dama wanda ya ta hankulan jarumai da suke zargin akwai wani abu a lamarin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka dalibai 2 da suka sace a Jami'a, ƴan sanda sun magantu

Daga cikinsu akwai Mista Ibu da Amaechi Muonagor da Junior Pope da Sisi Quadri da Ganiyu ‘Ogunjimi‘ Oyeyemi da sauransu.

Fati Slow ta yi bankwana da duniya

A wani labarin, kun ji cewa fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Fati Slow Motion ta riga mu gidan gaskiya a makon nan.

An sanar da rasuwar tsohuwar jarumar jiya Litinin 27 ga watan Mayu a kusa da kasar Sudan inda aka ce a can za a yi sallar jana'izarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel