Adam Zango Ya Bayyana Lalurar da Ta Same Shi Bayan Rabuwa da Matarsa

Adam Zango Ya Bayyana Lalurar da Ta Same Shi Bayan Rabuwa da Matarsa

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Adam Zango, ya magantu kan halin da yake ciki bayan mutuwar aurensa
  • Zango ya bayyana cewa yana samun kulawar likita a yanzu haka, sakamakon lalurar da ke damunsa kuma yana ba shi shawarwarin da ya kamata
  • Jarumin ya kuma janye kalamansa na baya cewa ba zai sake aure ba, inda ya ce yana bukatar mace domin kare martabar iyalinsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shahararren jarumin Kannywood, Adam A Zango, ya bayyana cewa yana samun kulawar likita kan cutar damuwa da ke damunsa bayan rabuwa da matarsa.

Bayan shafe tsawon watanni da dama ana fafatawa, daga karshe auren jarumin da matarsa, Safiyya Umar Chalawa, ya mutu a watan Afrilun 2023, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Adam Zango ya ce ya samu labarin matarsa tana shirin sake aure
Adam Zango Ya Bayyana Lalurar da Ta Same Shi Bayan Rabuwa da Matarsa Hoto: @adamzango
Asali: Instagram

A wata hira da sashin Hausa na BBC, Zango ya magantu kan fafatawarsa, inda ya ce hakan ya sanya ya ja baya sosai daga harkokinsa na yau da kullum da kokarin gano kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na kamu da cutar damuwa, Adam Zango

Ya magantu game da fuskantar matsaloli da yawa, wadanda suka hada da rikici da abokan aiki a masana'antarsu, matsalar dangi, da mummunar fassarar da al'umma ke yi wa kalamansa.

Ya yarda cewar wadannan matsalolin, sun yi sanadiyar da ya rasa alkibla da kuma fama da matsalar kwakwalwa.

Zango ya ce:

"Ina daya daga cikin wadanda ke fuskantar matsaloli a Kannywood, na fi kowa fuskantar haka. Idan mutum dari za su iya fadin abu a masana'antar nan, babu abin da zai faru, amma idan na farta kalma, wasu mutane za su fara fassarata ta baibai.

Kara karanta wannan

"Ku Riƙa Faɗin Alheri Kan Kasar Ku" Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga 'yan Najeriya

"Don haka, wadannan abubuwan sun sa dole na 'dan ja baya. Ina da matsala da wasu furudososhi da jarumai a masana'antar.
"Sannan ina da matsala da iyalina. Wadannan matsalolin sun sake daburta lamarina ta yadda na rasa alkibla. Bana yi ko tunani daidai.
"Don haka maimakon na zo soshiyal midiya ko fili na dunga aikata ba daidai ba yayin da nake tattare da damuwa, sai na zabi ja baya domin na farfado kafin na dawo daidai na ci gaba da harkokina.
"Ka san damuwa ma rashin lafiya ce da kanta wacce ke bukatar likita. Ina da likita da ke duba ni, sannan wannan, da addu'ar mahaifiyata, masoya da kaina, suna taimaka mani wajen farfadowa da sauki."

Ina bukatar kara aure don kare martabar iyalina, Zango

Da aka tambaye shi game da sulhu da matarsa, Zainab, jarumin ya ce har yanzu basu shirya ba, cewa ya samu labarin tana shirin aure.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Ya kuma yi karin haske kan furucinsa na baya cewa ba zai sake aure ba, yana mai cewa zuciya ce ta dibe shi.

Ya kuma ce yana bukatar sake aure don kare martabarsa da ta iyalinsa.

Zango ya magantu kan mace-macen aurensa

A wani labarin, mun ji a baya cewa Adam Zango, ya saki wani sabon bidiyo don yin karin haske kan maganganunsa na baya da yake cewa ya gama aure bayan sabani ya shiga tsakaninsa da matarsa.

A sabon bidiyon da ya saki wanda ke yawo a soshiyal midiya, Zango ya ce a kullun idan za a yi hira da shi sai an tabo bangaren rayuwar aurensa saboda kasancewar ya yi aure-aure da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel