Na fi kowani Bahaushe suna a duniya - Adam Zango (Bidiyo)

Na fi kowani Bahaushe suna a duniya - Adam Zango (Bidiyo)

Shahrarren mawaki kuma jarumin fina-finan Kannywood, Adam A. Zango ya jinjinawa kansa a matsayin bahaushen da ya fi yin fice cikin hausawan duniya.

A wata faifan bidiyo da ya wallafa a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa ta Instagram ya ce "Ni ne Bahaushen da na fi ko wane Bahaushe suna da masoya a duniya."

Adam Zago ya bayyana cewa ba shi ya gamo haka ba, masu bincike ne suka binciko hakan kuma ya samu labari.

Sai dai bai bayyana wadanda suka yi binciken ba har suka tabbatar da ya fi sauran hausawa shahara a duniya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo daga Senegal

Abinda da ya bayyana ga kowa shien Adam A Zango na da mabiya dubu 891 a shafin Instagram, mabiya 265,316 a Facebook, mabiya dubu 7.8 a shafin Tuwita.

Amma fitaccen jarumin fina-finan KAnnywood Ali Nuhu ya fi shi yawan mabiya a Instagram inda yake da mabiya sama da miliyan daya, mabiya 178,000 a Tuwita, mabiya milyan 1.6 a shafin Facebook.

Haka zakila jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau ta fi shi yawan mabiya a Instagram inda take da masoya miliyan 1.2, mabiya dubu 205 a shafin Tuwita, da mabiya 661,000 a Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng