Fitacciyar Jarumar Nollywood, Cynthia Okereke, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Fitacciyar Jarumar Nollywood, Cynthia Okereke, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Wata jaruma a masana'antar shirya fina-finan Nollywood, Cynthia Okereke ta riga mu gidan gaskiya jiya Talata da daddare
  • Abokin aikinta, Joseph Okechukwu ne ya tabbatar da rasuwarta a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 12 ga watan Yuli
  • Ya ce mutuwar ta girgiza shi saboda yana dab da aika mata da tikitin jirgi amma sai labarin cikawarta ya ci karo da shi

Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya watau Nollywood, Cynthia Okereke, ta riga mu gidan gaskiya.

Abokin aikinta a masana'antar shirya fina-fanai, Joseph Okechukwu, shi ne ya sanar da labarin mutuwarta ranar Laraba (yau) 12 ga watan Yuli, 2023.

Allah ya yi wa jarumar Nollywood, Cynthia Okereke rasuwa.
Fitacciyar Jarumar Nollywood, Cynthia Okereke, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: thenation
Asali: UGC

Mista Okechukwu ya wallafa Hoton marigayya jarumar tare kalaman yabo da faɗin kyawawan ɗabi'unta, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Haka zalika jarumin ya kuma nuna kaɗuwa da shiga matsanancin yanayi bisa rasuwar jarumar ba zato ba tsammani a daidai lokacin da suke kan aikin wani Fim.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Nada Tsohon Hadiminsa Mukami Mai Muhimmanci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Okechukwu ya kuma yi fatan ganin ya cinye jarabawar wannan babban rashi da aka yi a Nollywood, wanda a cewarsa ya yi matukar girgiza shi da ɗaga masa hankali.

Ya kara da cewa marigayya Cynthia Okereke mutumiyar kirki ce wacce ta iya zama da mutane, ga faran-faran da nuna soyayya a zamanin rayuwarta, Channels tv ta ruwaito.

Abinda jarumin ya faɗa game da mamaciyar

A kalamansa, Joseph Okechukwu ya ce:

"Ina miki fatan samun salama Nwanyi oma. Kalamai ba zasu iya bayyana halin da na tsinci kaina ba. A gaskiya ina dab da tura miƙi tikitin jirgi domin ki zo mu ƙarisa aikin da muka fara amma ba zato na ji labarin kin cika jiya da daddare."
"Ina addu'a Allah ya bani ikon fargaɗo wa daga halin da na shiga sakamakon wannan rashin, dama rayuwa juyi-juyi cewa, yau kai ne gobe ba kai bane."

Kara karanta wannan

Da Gaske Wike ‘Karamin Mahaukaci Ne’? Hadimin Atiku Ya Yi Martani Ga Furucin Fayose

"Na rasa kalaman ba zan faɗa, ina fatan ranki ya samu salama har zuwa ranar da zamu sake haɗuwa."

Wata Hajiya Daga Jihar Legas Ta Sake Rasuwa a Kasa Mai Tsarki

A wani labarin kuma Allah ya yi wa wata Hajiya mai shekara 70 a duniya rasuwa a ƙasa mai tsarki bayan kammala aikin Hajjin bana.

Hajiyar wacce ta fito daga jihar Legas ta koma ga mahaliccinta ne bayan ta yanke jiki ta faɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel