Kotun Musulunci Ta Tura Ƙarar Da Ake Yiwa Hadiza Gabon Zuwa Kotun Gaba Da Ita

Kotun Musulunci Ta Tura Ƙarar Da Ake Yiwa Hadiza Gabon Zuwa Kotun Gaba Da Ita

  • Ta ƙara tsawo a shari'ar da ake yi da shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon
  • Wata kotun shari'ar musulunci dake sauraron ƙarar ta tura ƙarar zuwa kotun gaba da ita domin cigaba da shari'ar
  • Ana zargin Hadiza Gabon da ƙarbe wa wani bawan Allah ƴan kuɗaɗen sa da zunan zata aure shi amma daga baya ta ƙi auren na sa

Jihar Kaduna- Wata kotun shari'ar Musulunci a Magajin Gari, Kaduna, ta ɗage ƙarar cin amana da yaudara da ake yiwa shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, zuwa babbar kotun shari'ar musulunci.

Alƙalin kotun, Isiyaku Abdulrahman, shine ya tura ƙarar zuwa babbar kotun shari'ar musulunci ta Tudun Wada, bayan lauyan mai shigar da ƙara ya buƙaci hakan. Rahoton Daily Nigerian

Gabon
Kotun Musulunci Ta Tura Ƙarar Da Ake Yiwa Hadiza Gabon Zuwa Kotun Gaba Da Ita Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

A yayin da yake tura ƙarar zuwa kotun gaba, alƙalin ya zargi lauyan mai shigar da ƙarar da son ɓatawa kotun lokaci.

Kara karanta wannan

"Nasarar Tinubu Ƙaddarar Ubangiji Ce, Kada Ku Yi Jayayya Da Ita" Aisha Buhari Ga Ƴan Najeriya

”Kana da zaɓi guda biyu. Na farko shine na kori ƙarar ko na miƙa ta zuwa wata kotun."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar alƙalin.

Ana dai ƙarar Hadiza Gabon ne bayan wani magidanci yayi ƙarar ta a kotu saboda ta ƙi yarda ta aure shi.

Magidancin mai suna Bala Musa, ya gagawa kotu cewa ya kashe maƙudan kuɗaɗe a kan jarumar tare da fatan cewa zata aure shi amma abu yaci tura.

"Ya zuwa yanzu na kashe mata kuɗi sun kai N396,000. Duk lokacin da na tambaye ni kuɗi, ina bata ba tare da wani jinkiri ba da fatan cewa za mu yi aure."

Hadiza Gabon tayi magana ta hannun lauyan ta, Bar. Mubarak Sani, inda ta musanta sanin Bala Musa da kuma yin soyayya tare da shi. Rahoton Gazettengr

Kara karanta wannan

Atiku Yayi Magana Kan Peter Obi, Ya Bayyana Babban Naƙasun Da Ya Yiwa PDP

Auren Mata 7: Babu Wanda Zai Yi Mun Uzuri, Adam Zango Ya Fadi Dalilinsa Na Cewa Ya Gama Aure

A wani labarin na daban kuma, fitaccen jarumin finafinan masana'antar Kannywood, Adam A. Zango yace ya gama yin aure a rayuwar sa.

Jarumin na masana'antar Kannywood dai ya taɓa yin aure har sau bakwai a rayuwar sa inda kuma duk zaman baya yin daɗi, daga ƙarshe sai a rabu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel