Auren Mata 7: Babu Wanda Zai Yi Mun Uzuri, Adam Zango Ya Fadi Dalilinsa Na Cewa Ya Gama Aure

Auren Mata 7: Babu Wanda Zai Yi Mun Uzuri, Adam Zango Ya Fadi Dalilinsa Na Cewa Ya Gama Aure

  • Jarumin fim Adam Zango ya saki sabon bidiyo don sassauta kalaman da ya yi a baya na cewa ya gama aure
  • Fitaccen dan Kannywood din ya ce ya auri mata daddaya har bakwai don haka mutane na masa wani kallo
  • Zango ya ce tun farko ya san cewa furucin da ya yi kan batun ba daidai bane amma yana bukatar samun sassauci a zuciyarsa

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam Zango, ya saki wani sabon bidiyo don yin karin haske kan maganganunsa na baya da yake cewa ya gama aure bayan sabani ya shiga tsakaninsa da matarsa.

A sabon bidiyon da ya saki wanda ke yawo a soshiyal midiya, Zango ya ce a kullun idan za a yi hira da shi sai an tabo bangaren rayuwar aurensa saboda kasancewar ya yi aure-aure da dama.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Adam Zango Ya Fallasa Sirrin Aurensa, Yace Zai Rabu da Matarsa, Ya Sanar da Dalilai

Adam Zango da matarsa
Auren Mata 7: Babu Wanda Zai Yi Mun Uzuri, Adam Zango Ya Fadi Dalilinsa Na Cewa Ya Gama Aure Hoto: @adamzango
Asali: Instagram

Na auri mata bakwai babu mai yi mun uzuri a duniyar nan, Adam Zango

Jarumin wanda ya auri matan aure daddaya har bakwai ya ce babu wanda zai yi mai uzuri a duniyar nan kan wannan batu sai Allah da ya halicce shi don haka ya fito ya yi magana don rage radadin da yake ji a zuciyarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga cikakken kalamansa:

"Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu, da fatan kowa yana cikin koshin lafiya. maganganun da zan yi basu da alaka da maganganun da na yi jiya, dan tsokaci ne zan yi a kan mutanen da suka yi bayanai a kan wannan abun, kowa fahimtarsa daban.
"Don haka, wasu daga cikin abokaina sun kira ni, wasu ma mun hadu da su, yan uwana, har malamai akwai wadanda aka hada ni da su, kuma suka yi mun nasiha suka nuna mun cewa ba daidai bane, a gyara.

Kara karanta wannan

Zuciyar Zinare: Shehu Sani Ya Tsinci Jinjiri a Titi, Ya Mayar Da Shi Dansa

"Don haka, kafin in yi maganganun jiya tsakani da Allah na san cewa ba daidai bane. Toh amma ni din dai Adamu Zango ba daidai nake da kowa ba.
"Idan wanda irin wadannan abubuwan suke faruwa da ni a gidana, zai iya jurewa, toh shine mutumin da ba shi da daukaka ta fannin harkar fina-finai ko kuma malanta ko siyasa. Don duk wadannan hanyar daukakar duk kusan iri daya ne.
"Toh wanda matsalarsa bata tsallake cikin gidansa ba zuwa unguwarsu ba, ko nine wallahi ba zan yi magana a ko'ina ba, ba ma soshiyal midiya ba. Kai babu mamaki ba banda wannan daukakar, babu mamaki ma matar da na aura ta farko da ta biyu ma ba mamaki da har yanzu tare da ita nake.
"Toh amma matsalar a nan shine, kallon da ake yi mun, na sani ban isa in wanke kaina a wurin wanda baya so na ba, ban isa ba. Amma ina da hanyoyi da zan iya tabuka wani abu domin ya rage mun zafin da nake ji ko abun da nake fuskanta.

Kara karanta wannan

Ango Ya Manta Da Amarya a Wajen Shagalin Bikinsu, Ya Mayar Da Hankali Kan Wayar Hannunsa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

"Saboda wannan kalmar da nake yi maku magana a kai, a Najeriya kai, duk kasashen da na je in dai zan je gidan rediyo ko dan jarida zai zo ya yi mun tambaya sai ya sako wannan magana a ciki. Toh ta yaya za ta iya barin zuciyata ko kwakwalwata kullun ana maimaita mun abu daya? kuma ba zan iya fitowa ba, ba zan iya fada ba, babu wani abu da zan iya yi saboda ba daidai bane in rika ba da labarin gidana.
"Amma kamar yadda na fada, daddaya har mata bakwai, babu wani mutum da zai yi mun uzuri a duniya tsakani da Allah. Sai Allah subahana wata'ala wanda shi kadai ne yake sane da komai.
"Wannan ne dalilin da yasa na yi magana, domin mutane su fahimci cewar ba daidai nake da sauran al'umma ba. Ni dan fim ne kuma na yi suna."

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Jama'a sun yi martani

iambashrr ya yi martani:

"Ana nan, ana nan zaku posting mana IV din aurensa. Muje zuwa……"

mamansadia ta ce:

"Ashe har sunkai bakwai???"

abdulmajeedgtahir ya yi martani"

"Mu dan Allah ya kyalemu muji da matsalolin Nigeria."

aysher_goje ta ce:

"Allah yabaka lafiya."

aishashalluh ta ce:

"Allah ya yayemasa danuwarsa dajamian mussulmin."

fatima.shariif ta ce:

"gaskiyane yasassauta kalamansa."

Na gama aure daga wannan, Adam Zango

A baya mun kawo cewa jarumi Adam Zango ya ce ya gama aure a duniya bayan ya kora matarsa gida saboda a cewarsa ta fi ba kasuwancinta muhimmanci a kan aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel