Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

  • Gwarzuwar jarumar masana’antar fina-finan arewacin Najeriya da kudu, Rahama Sadau, ta tanka Matashin da yace zai iya siyar da gonar gado a kanta
  • A wani kyakyawan hotonta da ta saka a shafinta na Facebook, mai tsokacin yayi rantsuwa da kwarankwatsa inda yace zai iya siyar da gonar gadonsa
  • Cike da barkwanci jarumar tayi masa martani inda yake ce masa kada ya siyar da gonar gadon, ya bar ta su noma tare

Fitacciyar jarumar fina-finai Raham Sadau, tayi martani ga matashin da yayi ikirarin cewa zai iya siyar da gonar gadonsa saboda ita.

Jarumar ta wallafa wani tsulelen hotonta ne a kafar yada zumuntar zamani ta Facebook inda tayi shigar matar aure.

Rahama Sadau
Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta. Hoto daga Rahama Sadau
Asali: Facebook

Duk da dai hoton an dauke shi ne yayin da ake daukar shiri mai dogon zango mai suna Matar Aure wanda gidan talabijin na Arewa24 ke haskawa, jarumar ta fito tsaf tamkar matar auren.

Kara karanta wannan

Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya

Wallafa hoton a shafinta Na Facebook babu dadewa masoyanta suka yi mata caa ida suke ta tsokaci tare da tofa albarkacin bakinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A tsokacin Ibrahim Abdullahi Sulaiman Shugaba, yace:

”A kan ki zan iya siyar da gonar gadonmu kwarankwatsa.”

Sai dai jarumar bata yi kasa a guiwa ba inda taje tayi masa martani da cewa:

“Ka bar mana mu yi noma tare…”

Ba wannan bane karo na farko da jarumar ke saka hotuna a kafafen sada zumuntar zamani ba har a yi mata tsokaci, sai dai bata cika kula masu yi mata tsokacin ba sakamakon zagi da sukar da take sha.

Shahararriyar jarumar tana yawan shan caccaka daga jama’a musamman ‘yan arewa kan irin yanayi da tsarin rayuwarta wanda suke ganin ya sha banban da nasu duk da kuwa cikakkiyar ‘yar arewa ce.

Kara karanta wannan

Mummunar Ambaliya Ta Kori Sarki, Mai martaba Ya Koma Kwana Cikin Mota

Jerin hotunan jaruma Rahama Sadau a India da suka janyo cece-kuce a makon nan

A wani labari na daban, Sanannen abu ne cewa jarumar fina-finai Rahama Sadau ta saba janyo cece-kuce a arewa.

A wannan makon wani sabon al'amari ya bayyana inda wasu suka dinga ganin sa a matsayin cigaba yayin da wasu ke tofin Allah wadai kan yanayin rayuwar jarumar.

A cikin makon nan kuwa, kwatsam sai ga jarumar ta wallafa wasu hotuna a shafin ta na Instagram inda ta bayyana tare da wasu jaruman fina-finan India maza ta dafa wasu.

Hakan babu shakka bai yi wa jama'a dadi ba inda suka fara cece-kuce tare da sukar irin tsarin rayuwar jarumar duk da Musulma ce kuma haifaffiyar 'yar arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel