Jerin hotunan jaruma Rahama Sadau a India da suka janyo cece-kuce a makon nan
- Sabbin hotunan jarumar fina-finai, Rahama Sadau sun bayyana inda suke daukan wani shiri tare da jaruman fim na India
- Sai dai wasu daga cikin hotunan sun bata wa jama'a rai ganin yadda ta dafa wani namiji tare da shigar ta wacce ta yi watsi da al'ada
- Tuni jama'a suka dinga sukar ta tare da janyo hankalin jarumar, inda wasu kuwa suka ce ba wannan ne karon farko da ta ke janyo wa kai magana ba
India - Sanannen abu ne cewa jarumar fina-finai Rahama Sadau ta saba janyo cece-kuce a arewa.
A wannan makon wani sabon al'amari ya bayyana inda wasu suka dinga ganin sa a matsayin cigaba yayin da wasu ke tofin Allah wadai kan yanayin rayuwar jarumar.

Asali: Instagram
Da farko dai jarumar ta fara da wallafa hotunan ta kusan makonni biyu da suka gabata inda ta bayyana a kasar India tare da jaruman kasar suna shirin fara daukar wani fim.
A take masoyan jarumar suka dinga tururuwar yi mata Allah ya sanya alheri tare da fata na gari kan wannan cigaban da ta samu a rayuwar ta.
A cikin makon nan kuwa, kwatsam sai ga jarumar ta wallafa wasu hotuna a shafin ta na Instagram inda ta bayyana tare da wasu jaruman fina-finan India maza ta dafa wasu.
Hakan babu shakka bai yi wa jama'a dadi ba inda suka fara cece-kuce tare da sukar irin tsarin rayuwar jarumar duk da Musulma ce kuma haifaffiyar 'yar arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng