Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya

Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya

  • Wata budurwa tayi suna a yanar gizo bayan ta bada labarin yadda saurayinta da suka shekara biyar suna soyayya yayi watsi da ita bayan ya koma ketare
  • Mutumin wanda ke fada mata cewa koyaushe ayyuka sun yi masa yawa, ya sanar da ita cewarta auri ‘yar kasar da yaje domin ya samu takardun zama kasar na dindindin
  • Jama’a da yawa sun yi kira ga budurwar kan cewa kada tayi Allah ya isa kan lamarin saboda koda ita ce haka zata yi ta samu zaman kasar

Wata matashiyar budurwar Najeriya mai amfani da suna @SandraOse_ tayi suna a yanar gizo bayan ta bada labarin yadda saurayinta mai suna Izuchukwu ya rabu da ita bayan kwashe shekaru biyar suna zuba soyayya.

Sandra
Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya. Hoto daga @SandraOse
Asali: Twitter

Tayi wallafa ne yayin yin martani ga mai wasan barkwanci Taaooma da yace jama’a su bayar da labarin cin amanarsu da aka taba yi.

Kara karanta wannan

Rahama Sadau Tayi Martani ga Matashin da Yace Zai Iya Siyar da Gonar Gado a Kanta

Saurayina yayi Wuff da Balarabiya

@SandraOse_ ta bayyana cewa bayan saurayinta ya koma ketare, Izuchukwu ya koma kullum bashi da lokacinta sai dai ita ta kira shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan shekaru biyu da barin kasar, ya tattaro kwarin guiwa inda ya sanar da ita cewa ya aura balarabiya saboda yana son shaidar zama ‘dan kasar.

Ta ce:

“Duk inda kake, Ubangiji zai cigaba da yin maganin ka.”

Jama’a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin da aka yi mata.

@engineershegun yace:

“Ko kina da katin zama ‘yar kasar ne.”

@demola2009 yace:

“‘Yar uwa zai yuwu har yanzu kina ransa lokacin da ya tara dukiya a can. Babu fa sauki ka rabu da Budurwa kan kana son zama ‘dan kasa.”

@_tobby0 yace:

“Hahahhaha, kin san ina amfani da wannan manhajar fa Sandra.”

Kara karanta wannan

Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure

@KayciOkeke yace:

“Budurwa bar wannan batun. Ubangiji ba zai saka miki kan Izuchukwu ba. Bari in tambaye ki, da a ce ya bar ki kina jira tare da yaudarar ki ba tare da ya fada miki abinda yayi ba fa? Saurayin nan fa yana son ki amma wasu lokutan gara cikar buri da soyayya. Na ji miki ba dadi dai.”

@Valentinon1483:

“Abun dariyar ko ita ta samu dama haka zata yi. Ja’ira.”

@gentlenlizz yace:

“Idan da kin fahimce shi da baki dinga fadin hakan ba. Da ‘Dan uwanki ne fa? Ya zaki yi?”

Baturiya ta kashewa saurayinta makudan kudi, tana shirin zuwa Najeriya aurensa

A wani labari na daban, wata baturiya yar shekara 60 ta bayyana dan Najeriya, Peter, dan shekaru 22 a matsayin masoyin da bata taba haduwa da mai son ta irinsa ba tun lokacin da ta fara soyayya a rayuwarta.

Matar ta bayyana hakan ne a shirin Dr. Phil Show.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel