Shekara 2 da Barin Ofis, Magu Ya Bayyana Dalili 1 da Ya sa Aka Fatattake Shi daga EFCC

Shekara 2 da Barin Ofis, Magu Ya Bayyana Dalili 1 da Ya sa Aka Fatattake Shi daga EFCC

  • Tsohon Shugaban hukumar EFCC na rikon kwarya, Ibrahim Magu ya samu lambar yabo na musamman
  • Kungiyar dalibai mata na Arewacin Najeriya ta karrama Magu saboda kokarin da ya yi a Hukumar EFCC
  • Magu ya ji dadin karbar lambar yabon, yace an yi waje da shi ne saboda yana yaki da rashin gaskiya

Abuja - Ibrahim Magu wanda ya rike jagorancin hukumar EFCC na rikon kwarya, ya yi maganar barinsa ofis a wajen wani taro da aka yi a garin Abuja.

Tribune tace Ibrahim Magu ya yi jawabi a wajen taron da kungiyar dalibai mata na Arewacin Najeriya suka shirya domin karrama shi a ranar Lahadi.

Da yake gabatar da jawabi, tsohon shugaban hukumar ta EFCC yace ya rasa mukaminsa ne dalilin yakarsa da marasa gaskiya suka dawo suka yi.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Magu yake cewa hakan ta faru ne saboda yana neman fallasa su a hukumar.

“Rashin gaskiya ce ta dawo ta yake ni, amma ina mai farin cikin yadda abubuwan da suke faruwa daga bayan nan suke nunawa ‘Yan Najeriya gaskiya.

- Ibrahim Magu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Magu ya samu wakilcin yaronsa

Jaridar The Cable tace Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu ne ya wakilci mahaifinsa a wajen wannan taro da kungiyar dalibai mata suka shirya a jiya.

EFCC.
Shugaban kasa tare da Ibrahim Magu Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

A madadin mahaifinsa, Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu ya godewa ‘yan kungiyar da suka karrama shi, yana mai murnar samun wannan lambar yabo.

Meyasa aka karrama Magu?

Kakakin wannan kungiya ta matan yankin Arewacin Najeriya da ke karatu a jami’o’i, Aisha Nasir tace sun karrama Magu ne saboda irin hidimar da ya yi.

Aisha Nasir take cewa Ibrahim Magu ya yi namijin kokari wajen yaki da rashin gaskiya a lokacin yana rike da EFCC, ya yi abin da ba a taba tunanin za a iya ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

“Yaki da rashin gaskiya nauyi ne da ya rataya a sauke ba tare da nuna banbamcin siyasa ko wani fifiko ba.
Magu ya jawo abin yabo daga Afrika da kasashen Duniya saboda ya yaki da abin da ya hana cigaba da bunkasar tattalin arzikin Afrika.”

- Aisha Nasir

A ‘yan kwanakin nan ne kotu ta wanke Magu daga zargin da ake yi masa cewa ya yi amfani da Fasto Emmanuel Omale wajen sayen gidaje a Dubai.

Kasafin kudin 2023

Kuna da labari har gobe Gwamnatin Muhammadu Buhari tana bukatar ta karbo tulin bashi kafin a iya aiwatar da ayyuka a shekarar 2023 mai zuwa.

A kan haka Sanata Betty Apiafa tace dole sai an yi maganin tsagerun da ke satar danyen fetur din Najeriya sannan a dage wajen samun kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel