Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

  • Dakarun sojin saman Najeriya karkashin Operation Whirl Punch sun halaka rikakken ‘dan bindiga Ali Dogo da wasu mukarrabansa
  • Kamar yadda aka gano, Dogo da mayakansa sun yi hijira daga jihar Niger zuwa karamar hukumar Giwa da ta jihar Kaduna
  • Sun samu masauki a gidan wani Alhaji Gwarzo amma suna tsaka da taro jirgin NAF ya ragargajesu inda duk wanda ke gidan ya sheka lahira

Giwa, Kaduna - Dubun Shugaba kuma gagararren ‘dan ta’addan jihar Kaduna, Ali Dogo, ta cika inda sojoji suka aika shi lahira tare da wasu mayakansa sakamakon luguden wuta ta jiragen yaki da aka yi musu a karamar hukumar Giwa ta jihar.

An gano cewa dakarun rundunar Operation WHIRL Punch ne suka a kwanakin karshen mako da ya gabata.

Kara karanta wannan

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Jiragen NAF
Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo. Hoto daga Defense Hedquarter
Asali: Facebook

Wata majiyar tsaro ta sanarwa PRNigeria cewa Dogo da mabiyansa sun tsero daga jihar Niger zuwa karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna sakamakon luguden wutan da aka matsanta musu a maboyarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan ta’addan sun samu maboya ne a gidan wani Alhaji Gwarzo a Yadi dake karamar hukumar Giwa kafin a halaka su.

Majiyar tace:

“Abun takaici ga Yellow da mayakansa, yayin da suke taro, jiragen NAF sun yi lugude a gida Alhaji Gwarzo inda duk wanda yake gidan aka halaka shi har da Yellow.”

- Majiyar tace.

A wani bangare, luguden wuta mabanbanci da aka yi shi kan wan sansanin ‘yan ta’addan dake da nisan kilomita 33 arewa maso yamma na Mando a jihar Kaduna, ya zama ajalin wasu ‘yan ta’addan.

“Bayan bayyanan sirri kan cewa shugabannin ‘yan ta’addan da sojojinsu suna taro a karkashin bishops a wurin, an kai wa yankin samame wanda hakan yayi ajalin ‘yan ta’addan masu tarin yawa.”

Kara karanta wannan

Zargin Sakin ‘Yan Boko Haram 101 daga Magarkamar Kirikiri Ya Tada Hankula

- Majiyar tsaron tace.

Mai magana da yawun sojin saman, Edward Gabkwet ya tabbatar da cewa luguden wutan da suke yi yana daga cikin umarnin shugaban sojin sama, Oladayo Amao.

Yace rundunar tare da hadin guiwar sojin kasa da sauran hukumomin tsaro zasu hada kai wurin kawo karshen ta’addanci da sauran laifuka a dukkan arewa maso yamma.

Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara

A wani labari na daban, Bello Turji mashahurin ‘dan bindiga ne da ya addabi yankuna da yawa na jihar Zamfara. Sai dai duk da shahararsa, kiyasi a kan tsaro wanda Zagazola Makama ya bayyana ya lissafo wasu kwamandojin ‘yan bindiga biyar da suka fi Bello Turji hatsari da shu’umanci a jihar Zamfara.

Aleru na zama ne a Munhaye dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kuma shi ne da alhakin hare-hare masu yawa a kananan hukumomin Tsafe da Gusau.

Suna addabar jihohi masu makwabtaka kamar Katsina tare da manyan hanyoyin Gusau zuwa Funtua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel