Ayiriri: Shirin Shagalin Auren Rukayya Dawayya da Afakallah Ya Kankama

Ayiriri: Shirin Shagalin Auren Rukayya Dawayya da Afakallah Ya Kankama

  • Shirin auren jaruma Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya da Isma’il Na’abba wanda aka fi sani da Afakallah yayi nisa
  • Kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa da mujallar fim, daga yanzu koyaushe za a iya jin daurin auren masoyan junan
  • Sai dai majiyar tace da farko masoyan daura aure zasu yi kawai babu shagali, amma sun matsanta a yi musu dina

Shekara na zuwa karshe aurarraki na cigaba da yawaita. Hankulan wasu ‘yan fim ya koma kan aure kuma ana ta jiran auren Hajiya Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya da shugaban Hukumar tace fim na Kano, Isma’il Na’am ba wanda aka fi sani da Afakallahu.

Rukayya Dawayya
Ayiriri: Shirin Shagalin Auren Rukayya Dawayya da Afakallah Ya Kankama. Hoto daga @dawayya
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Mujallar fim ta samu zantawa da wasu a masana’antar Kannywood duk da sun bukaci a sakaya sunayensu kan tsumayen bikin da suke yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiya mai karfi ta bayyana cewa shirin auren masoyan junan.

A batun auren, majiyar ta sanar da cewa:

“Ba yanzu aka fara batun auren ba. Ko makaho a Kannywood ya san akwai soyayya a tsakanin Afakallah da Dawayya.
“Abu ne da aka jima ana yi a kasan kasa ba tare da an bayyanawa duniya ta sani ba. A yanzu da aski yazo gaban goshi ne yasa Rukayya ta fara dora hoton Afakallah a status na WhatsApp, TikTok da Instagram tare da bayanai masu nuna alamun soyayya dake da karfin gaske.”

Ta cigaba da cewa:

“Akwai batun auren kuma a koyaushe daga yanzu za a iya yinsa.
“Duk da an ce ba wani taro za a yi ba. Za a dai daura aure amarya ta tare.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

“Mune muka dage sai an yi dina. Dawayya ba karamar jaruma bace, shima Oga kowa ya san matsayinsa don haka za mu yi biki sosai.
“Suna kammala shirin da suke yi za a ji sanarwar daurin auren. Ba abu ne da za a boye ba.”

Jaruma Rukayya Dawayya zata amarce, ta fitar da hoton angon

A wani labari na daban,fitacciyar tsohuwar jarumar masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya, za ta amarce.

Legit.ng ta gano hakan ne bayan jarumar ta wallafa hoton masoyinta wanda kuma shine ake fatan ya zama angon, a shafinta na Instagram.

Wanda ta wallafa hoton sa tare da kwarara masa addu'ar masoyan, shine shugaban hukumar tace fina-finai, wato Afakallahu.

Babu jimawa da wallafar masoyanta suka dinga yi mata fatan alheri inda ta dinga amsa addu'o'in da aka yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel