'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

  • Musulmi mabiya akidar shia' a Najeriya sun maka IGP Usman Baba Alkali da CMD na asibitin kasa a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja
  • 'Yan shi'an sun bukaci alkali da ya aike IGP da CMD din zuwa gidan yari kan yadda suka take tare da mitsike hukuncin da ya yanke
  • 'Yan kungiyar sun zargesu da hana gawawwakin mambobinsu wadanda 'yan sanda suka bindige a ranar 22 ga watan Yulin 2019 a Abuja

Mambobin kungiyar IMN, Musulmai maboya akidar Shi’a, sun koma kotu suna bukatar a aike Sifeta Janar na ‘yan sandan Najeriya da Daraktan asibitin kasa na Abuja, gidan kurkuku.

Kungiyar tace hakan ya zama dole ne saboda sun ki bin umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja wacce tayi umarnin a saki gawawwakin mambobin kungiyar da aka halaka a ranar 22 ga watan Yulin 2019, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

IGP Alkali
'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wadanda lamarin ya ritsa dasu suna zanga-zanga ne kan cigaba da garkame shugaban IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenah da jami’an tsaro ke yi duk da kotu tayi umarnin a sake shi.

Wata mamban kungiyar na fannin ilimi, Halima Aliyu, ta sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja ranar Litinin inda ta mika takardun kotun ga manema labarai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fom din kotun da magatakardan babban kotun tarayya yasa hannu, wani bangaren ta yace:

“Ku sani, wanda ya kawo kara ya bukaci a aike masu karya dokar zuwa gidan gyaran hali sakamakon karya dokar kotu da aka yi ta ranar 29 ga watan Yunin 2020.”

Aliyu tace kotun ta bada umarnin sakin gawawwakin.

'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamnan APC a Kaduna ya fadi dan takarar shugaban kasan da ya fi cancanta a zaba

A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa da yammacin nan shi ne na angamar Musulmi mabiya Shi'a da jami'an tsaro a garin Zaria.

'Yan shi'an sun fito tattaki da zanga-zanga inda bayanan da Legit.ng ta tattaro suka bayyana cewa sun fara tun daga Masallacin 'yan kaji da ke cikin kasuwar Sabon Gari a Zaria.

Ganau ba jiyau ba sun tabbatarwa da Legit.ng yadda 'yan Shi'an suka gangara a kasa suna tattakinsu tare da toshe hannu daya na tagwayen titin da ke PZ a Zaria.

Babu dadewa da hakan ne aka ga 'yan Shi'an sun fara kone-konen tayoyi a kan titin duk kuwa da cewa sun yi ikirarin zanga-zangar lumana suka fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel