Kannywood: Hotunan Hauwa Ayawa da Umar Gombe Ya Haddasa Cece-kuce A Soshiyal midiya

Kannywood: Hotunan Hauwa Ayawa da Umar Gombe Ya Haddasa Cece-kuce A Soshiyal midiya

  • Wasu sabbin hotunan jaruman kannywood, Umar Gombe Da Hauwa Ayawa sun bayyana a shafukan soshiyal midiya
  • Hotunan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausan sun fi kama da wanda ake kira da ‘hotunan kafin aure’
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu, yayin da wasu suka yi san barka, wasu na hasashen shirin fim ne

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wasu sabbin hotuna na manyan jaruman Kannywood, Hauwa Ayawa da Umar Gombe.

Hotunan wadanda tuni suka karade shafukan soshiyal midiya ya nuno jaruman sun yi tsayuwar daukar hoto irin na masu shirin yin aure.

Hauwa Ayawa da Umar Gombe
Kannywood: Hotunan Hauwa Ayawa da Umar Gombe Ya Haddasa Cece-kuce A Soshiyal midiya Hoto: falalu_a_dorayi
Asali: Instagram

Babban darakta kuma jarumin masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya wallafa hotunan a shafinsa na Instagram dauke da wasu rubutu da ke nuna jaruman za su shiga daga ciki.

Ya bayyana 6 ga watan Oktoba a matsayin ranar da wannan alkawari zai cika.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji Sun Harba Manyan Makamai Kan 'Yan Ta'adda, Da Yawa Sun Zarce Lahira

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mabiya shafin nasa da dama sun yi musu fatan alkhairi yayin da wasu da dama ke ganin kawai shirin fim ne. harma wasu sun yi hasashen cewa ci gaban ‘Gidan Badamasi’ wani shiri mai dogon zango ne.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Allah Ya sanya alkairi Umar Gombe & Hauwa AYawa. Komai yana da lokacin sa.
“6 October, 2022.”

Jama’a sun yi martani

mufeeda_rasheed1 ta yi martani:

"Anyaa ba gidan badamasi bane?"

azima_gidan_badamasi_ ta ce:

"Ameeen summa ameen Baba ."

safiyyahbabashe ta yi martani:

"Allah sa albarka."

momee_gombe ta ce:

"Allah Ya basu zaman lfy baba ."

his_queen202_ta yi martani:

“Dagaske ko wasa…”

faruk_sayyadi ya ce:

“Wannan hadi ya yi. Daman mun Dade mu na jira.”

kamal_a_zango ya yi martani:

“Masha Allah Alhamdulillah. Allah yasanya alkhairi bro.”

__kubrah_kubsy_ta ce:

“Masha AllahAllah ya sanya alkhairi ♥️.”

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka

Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

A wani labarin, mun ji cewa jama’a sun shiga rudani bayan bayyanar wasu hotuna na manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja da Momee Gombe a soshiyal midiya.

A cikin hotunan wadanda tuni suka yadu a shafukan sadarwa, an gano jaruman biyu cikin shiga da ta fi kama da ta sabbin ma'aurata kuma sun yi tsayuwar daukar hoto sak irin na amarya da ango.

Wannan al’amari ya jefa mutane cikin shakku, yayin da wasu ke ganin shirin fim ne, wasu kuma sun yi fatan Allah yasa hakan ya zamo gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel