Jarumai goma da suka fi kowa kudi a masana'antar Kannywood
1. Ali Nuhu
Ali Nuhu jarumi ne kuma darakta ne a masana'antar Kannywood, wanda aka fi sani da Sarki Ali, ambasada ne na akalla kamfanoni guda bakwai a Najeriya cikinsu akwai Glo, Omo, Samsung da dai sauransu.
Bayan kungiyar Kannywood da Ali Nuhu yake taka rawa akwai kuma kungiyar Nollywood dake kudancin kasar nan wadda dan wasan yake nuna bajintarsa a can. Jarumin yayi fina-finai a kamfanin Kannywood sama da guda dari, irinsu Jinin Jikina, Matar Aure, Gani Gaka, Mansoor, Adamsy, Dawo Dawo daidai sauransu.
Sannan kuma jarumin an nuna shi a fina-finan Nollywood irinsu, Last Fight to Abuja, Memories of my Heart, Beautiful Soul, Hamza, Brothers Apart, Widow Tears, Royar Treasure da dai sauransu.
Wannan dalili ne yasa jarumin ya zama na farko a cikin jaruman da suka fi kudi a masana'antar ta Kannywood.
2. Adam A Zango
Adam A Zango mawaki ne kuma jarumi, wanda aka fi sani da Prince Zango. Yana da wani katafaren gida a jihar Kaduna, yana kuma da masoya da yawan gaske.
Adam A Zango ambasada ne na kamfanin MTN, a shekarar 2016 Adam A Zango ya wallafa wani rubuta a shafinsa na Instagram cewar ya bar fim, inda ya ce zai koma bangaren waka da shirya fina-finai, sai dai kuma wani labari ya fito daga makusantansa cewa yayi amai ya lashe.
Zango yayi fina-finai shima sama da guda dari irinsu Nas, Gwaska, Basaja, Gamdakatar da dai sauransu. Wannan ne ya sanya jarumin Adam A Zango ya zama na biyu a cikin jerin jaruman.
3. Dauda Kahutu Rarara
Dauda Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, mawaki ne na siyasa, wanda yake da kusanci da manyan 'yan siyasa na kasar nan, an bashi mukamin babban darakta na mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zaben shugaba Buhari a shekarar 2019.
Wannan suna da kuma daukaka da Dauda Kahutu Rarara yayi shine yasa ya zama mutum na uku a cikin jerin wadanda suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood.
4. Nura M Inuwa
Nura M Inuwa mawaki ne a bangaren soyayya, yana daya daga cikin masu kudin kungiyar Kannywood, yana fitar da wakoki masu yawan gaske kowacce shekara, kyakkyawa ne, kuma shine na hudu a cikin jerin jaruman.
5. Halima Atete
Halima Atete jaruma ce a masana'antar Kannywood, ita ce ta biyar a cikin jerin wadanda suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood, sannan kuma ita ce ta daya a cikin jarumai mata.
KU KARANTA: Ke duniya: Mutanen da suka je taimakon wanda mota ta buge, sun sace kudin jikinsa karkaf sun barshi cikin jini
6. Sani Musa Danja
Sani Musa Danja wanda aka fi sani da Sani Danja shine ya zo matsayin na shida a cikin jerin jaruman, jarumi ne kuma mawakin siyasa, yana da wani katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja.
7. Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da Gambo Uban Tani, yana daya daga cikin wadanda suka fi kowa iya kwalliya a cikin jaruman Kannywood, sannan ya karbi lambar yabo ta gwarzon dan wasa a kungiyar, hakan ya sa ya zama na bakwai a cikin jerin jaruman.
8. Nafisa Abdullahi
Nafisa Abdullahi ita ce ta zo ta takwas a cikin jerin jaruman da suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood, sannan kuma ita ce ta biyu a cikin jarumai mata a kungiyar.
9. Hadiza Gabon
Hadiza Gabon jaruma ce ita ce kuma ta zo ta tara a cikin jerin jaruman sannan kuma ita ce ta uku a cikin mata. Tana daya daga cikin manyan jaruman da suke son ganin sun taimakawa al'umma.
10. Aisha Aliyu Tsamiya
Aisha Aliyu Tsamiya wacce aka fi sani da Aisha Tsamiya, kyakkyawa ce ta gaban kwatance tayi fina-finai masu tarin yawa, ita ce ta samu nasarar zuwa ta goma a cikin jaruman sannan kuma ita ce ta zo ta hudu a cikin jarumai mata na masana'antar ta Kannywood.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng