“Za Mu Taimake Shi”: Ali Jita Ya Magantu Kan Halin da Adam a Zango Yake Ciki
- Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki
- Ali Jita ya ce Adamu mutumin kirki ne kuma lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk su fito su ja shi a jika tare da neman mafita
- Idan ba a manta ba, mawaki Zango ya saki wani bidiyo wanda yake nuna irin butulcin da ya ce wasu 'yan Kannywood sun yi masa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki.

Asali: Twitter
Ali Jita wanda ya yi martani kan bidiyon Zango a shafinsa na TikTok a ranar safiyar ranar Litinin, ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan Kannywood su taimaki Adam A Zango.

Kara karanta wannan
"Ban son zama ubangida" Malam El-Rufa'i ya mayar da martani kan abin da ke faruwa a Kaduna
"Daukaka ba alkairi ba ce" Adam A Zango
Mawaki Zango ya dauki wani faifan bidiyo wanda ya fadawa duniya irin jarabawar rayuwar da yake fuskanta, kamar yadda shafin Arewa Focus ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na ba mutane da dama gudunmawa a Kannywood, amma basu taba yabo na ba sai dai su yabi wani daban saboda ni wulakantacce ne a wajensu.
"Daukaka ba alkairi bace, kullum kana nunawa duniya kana da kudi kuma ba ka da matsala, amma a zahirance kafi kowa fuskantar kalubale, kuma babu hali ka fito ka fada."
Wadanda Adam Zango ya taimaka a Kannywood
Adam Zango ya lissafa wadanda ya ba kyautar mota a masana'antar da suka hada da Falalu A Dorayi, Sadiq N. Mafia, Tahir I. Tahir, Abubakar Sani, Kabiru, Rabiu, Umar Big Show.
Wadanda ya taimaka suka samu daukaka a Kannywood kamar yadda ya zayyana, sun hada da:

Kara karanta wannan
Adam A Zango ya fitar da sabon faifan bidiyo kan halin da ya ke ciki, ya yi godiya
"Fati Nijar, Nazifi Asnanic, Zainab Raga, Zainab Indomie, Ali Jita, Isah Feruskan, Umar Big Show, Ado Gwanja, Ussaini Danko, Umar M. Shareef da Sadiq Sani Sadiq."
"Adamu mutumin kirki ne" - Ali Jita
A wannan gabar ne, mawaki Ali Jita ya yi martani kan kalaman na Zango, inda ya gasgata dukkanin abin da ya fada tare da cewa:
"Adamu mutumin kirki ne kuma zuciyarshi tana da kyau, ba shakka ya taimake ni da sauran wadanda ya lissafa. Ina amfani da wannan dama in bashi hakuri a madadinmu gaba daya.
"Ina ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk mu fito mu ja Adamu a jiki, mu gane matsalolin da aka samu a baya domin a gyara su."
Ali Jita ya yi nuni da cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, don haka za su zauna da Zango a kungiyance domin yi wa dukkanin tufkar hanci.
"Adamu na cikin koshin lafiya" - Ali Nuhu
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jarumi Ali Nuhu ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook da ta nuna cewa jarumi Adam A Zango na nan cikin koshin lafiya.
Ali Nuhu ya yi wannan sanarwar ne biyo bayan rubututtuka da bidiyo da mawaki Zango ya wallafa a soshiyal midiya wanda yake nuna irin mawuyacin halin da yake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng