Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Hotunan Matashin Ɗansa Dake Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama'a

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Hotunan Matashin Ɗansa Dake Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama'a

  • Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Ali Nuhu, mahaifi ne mai alfahari da dan shi wanda ya bayyana Ahmad a matsayin kwarrren dan kwallon kafa
  • Ali ya bayyana hoton matashi Ahmad wanda ke shirin fita filin wasa a wani wasan da zasu yi a Ingila a shafinsa na Instagram
  • Jarumin ya yi wa 'dansa fatan alheri, kuma 'yan Najeriya sun dinga kururuwa zuwa sashin tsokaci inda suke bayyana birgesu da yayi

Sanannen jarumin masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana hotunan zabgegen saurayin 'dan shi, Ahmad, wanda ke wasan kwallon kafa a Ingila.

Mahaifin mai cike da alfahari da 'dan shi, yayi masa fatan alheri yayin da ya wallafa hoton matashin yana sanar da cewa yana shirin fita wasa ne.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Ali Nuhu and Ahmad
Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Hotunan Matashin Ɗansa Dake Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama'a. Hoto daga @realalinuhu
Asali: Instagram

Ali Nuhu ya wallafa hoton matashi Ahmad a shafinsa na Instagram kuma kara da bayanai masu kara karfin guiwa a wasan da zasu buga.

Ya kara da bayyana wani hoton matashin 'dan kwallon, ga shi a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya sun yabawa Ali Nuhu da 'dansa mai kwallon kafa

Ma'abota amfani da kara sada zumuntar zamanin na duniya sun dinga tururuwar yin tsokaci karkashin wallafar Ali Nuhu kan 'dan shi tare da rubuta kalaman sam barka.

Legit.ng ta tsamo muku wasu daga cikin tsokacin.

Deejay_kz: "Gwarzon duniya a nan gaba."
Eeshaq678: "Zaka samu alfahari wata rana da izinin Ubangiji."
Zuwairatummumaryam: "Barakallahu MashaAllah, wannan yaron na girma da hanzari. Ina fatan ka daukaka a duk abinda ka saka gaba a rayuwarka. Amin."
Tahansy: "A bayyane kamanninku suke. Karin ni'ima ga iyalanka Ya Rabbi."

Kara karanta wannan

Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila

Ibrokhan20: "Ina fatan zai yi nasarar zama fitaccen 'dan kwallo."
Aleemlah: "Wannan yaron ya yi matukar kama da mahaifinsa, hazakarsu a jini take, nan babu dadewa 'yan mata zasu fara bibiyarsa."

Hotuna da bidiyo: Jaruma Nafisa Abdullahi zata kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata

A wani labari na daban, fitacciyar jarumar masana'antar Kannywood kuma 'yar kasuwa, Nafisat Abdullahi, za ta kaddamar da katafaren kamfanin yin jakunkuna mata.

Jarumar ta wallafar sanarwar a shafinta na Instagram inda yake biye da bidiyo da hotunan jakunkunan mata 'yan kwalisa.

Kamar yadda jarumar ta sanar, ta yi watanni tana amfani da jakunkunan kamfanintan amma sai yanzu ne ta ga lokaci yayi da zata tallata su ga duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel