Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila

Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila

  • 'Yan Najeriya a soshiyal midiya sun bayyana martani daban-daban kan mutuwar Sarauniya Elizabeth II ta Ingila
  • Idan za a tuna, basarakiyar ta kwashe sama da shekaru 70 tana kan karagar mulkin kafin ta rasu a ranar Alhamis
  • Jim kadan bayan rasuwarta, 'yan Najeriya sun bayyana hotunan atamfofi masu dauke da hoton sarauniyar matsayin ankon bikin mutuwarta.

In har a wurin nishadi ne, ba a wuce 'yan Najeriya kuma ko da ake cikin tsananin makoki da kunar mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth, sun cigaba da ba mutane dariya da salonsu.

Sarauniya Elizabeth II ta rasu a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 yayin da take da shekaru 96 a duniya.

Sarauniyar Ingila
Hotunan Atamfofin da 'Yan Najeriya Suka Fitar Matsayin Ankon Bikin Mutuwar Sarauniyar Ingila. Hoto daga @theroyalfamily, @goldmyne
Asali: Instagram

Kamar yadda dai aka saba a Najeriya, ana yin ankon atamfa ko leshi a yayin bukukuwan mutuwa wanda 'yan uwa da abokan arzikin mamatan ke sanyawa.

Kara karanta wannan

Kada Wani Bakin Fata Yayi Jimamin Mutuwar Sarauniya Elizabeth, Trevour Sinclair

Toh a wannan ma ba a bar 'yan Najeriya a baya ba, sun yanke hukuncin fitar da nako mai hoton sarauniyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shafin @goldmyne ne suka wallafa a Instagram cike da barkwanci yayin da ake bayyana kudin ankon ga masu son siya.

Duba wallafar:

'Yan Najeriya sun yi martani kan ankon mutuwar Sarauniya

pisax_marcel:

"Don Allah ya za a yi in siya har da Aso Oke da cikakken kallabin? Tamkar mahaifiya take a wurina."

realhonestmax:

"Komai zan iya yi saboda sarauniyarmu, nawa ne atamfar?

goalgetter3571:

"Bai fa cika ba saboda ba a hada da kudin visa da na jirgi ba."

unknown_hf.xx:

"Mutane sun fara haukacewa a kan wannan lamarin."

Kyawawan Hotunan Lokuta da Rayuwar Marigayiyar Sarauniya Elizabeth II

A labari na daban, Ingila ta fada makoki a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumban 2022 bayan labarin mutuwar sarauniya Elizabeth Alexandra Mary wacce ta kasance sarauniyar da ta fi kowanne sarki dadewa a kujerar sarautar Birtaniya.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Biloniyoyi Dangote da Tony Elumelu Suka Dauka Hankalin Jama'a a Filin Jirgi

Mahaifiya kuma kakar an haifeta a ranar 21 ga watan Afirilin 1926 a titin Bruton dake Landan, UK ga tsohon Duke din York, Yarima Albert da matarsa Elizabeth Bowes-Lyon.

Kamar yadda takardar da fadar Buckingham ta fitar ta bayyana,sarauniyar ta tabbata basarakiyar da tafi dadewa a kujerar tun a 2015 yayin da ta wuce shekarun da Sarauniya Victoria tayi a kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel