Hotuna da bidiyo: Jaruma Nafisa Abdullahi zata kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata

Hotuna da bidiyo: Jaruma Nafisa Abdullahi zata kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, za ta kaddamar da katafaren kamfanin ta na hada jakunkunan mata 'yan kwalisa
  • Kamar yadda jarumar ta sanar a Instagram, ta fara hada jakunkunan tun wasu watanni da suka gabata amma ita ke amfani da kayan ta
  • A cewarta, zata kaddamar da su a ranar 14 ga watan Augusta wanda zata iya cewa yana daga cikin burikanta da ta dade tana raino

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitacciyar jarumar masana'antar Kannywood kuma 'yar kasuwa, Nafisat Abdullahi, za ta kaddamar da katafaren kamfanin yin jakunkuna mata.

Jarumar ta wallafar sanarwar a shafinta na Instagram inda yake biye da bidiyo da hotunan jakunkunan mata 'yan kwalisa.

Kamar yadda jarumar ta sanar, ta yi watanni tana amfani da jakunkunan kamfanintan amma sai yanzu ne ta ga lokaci yayi da zata tallata su ga duniya.

Nafisat Abdullahi
Hotuna da bidiyo: Jaruma Nafisa Abdullahi zata kaddamar da kamfanin yin jakunkunan mata. Hoto daga @nafeesat_official
Asali: Instagram

Kamar yadda wallafarta ta nuna karkashin bidiyonta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani yanayi mai muhimmanci nake shiga idan na ganni ina yi abinda nake mafarki.
"Daya daga cikin tsofaffin burikana shi ne in samu jakunkuna da suka fito daga gareni, in iya daukar jakar zuwa kowanne sashi na duniya dauke da sunana. Na samu nasarar yin hakan shekarar da ta gabata.
"Eh, amma ban ji cewa wancan lokacin bane ya kamata in nunawa duniya NAAF Luxury. Bayan yin gaba da komawa baya tare da yanke hukuncin yi, zaben launikan da suka dace, na shirya gabatar muku da su duka!!!"

Bayyanar bidiyo da hotunan motar jaruma Nafisa Abdullahi ta N30m ta dauka hankali

A wani labari na daban, wasu sabbin bidiyo da hotuna na jaruma Nafisat Abdullahi tana shagalinta da tsadajjiyar mota ya dauka hankulan jama'a masu tarin yawa.

Ba kuwa komai bane ya dauka hankalin jama'a ba illa zukekiyar mota da aka ga jarumar ta fizgo wacce ta kasance 'yar yayi wacce ba kowa ke iya hawanta ba sai wane da wane ke iya hawan irinsu.

Shafin labaran Kanyywood na Twitter sun yi kiyasin farashin motar inda suka ce a kalla ya kai kimanin naira miliyan 30 a wata wallafa da suka yi a shafinsu inda suka wallafa bidiyon.

"Tauraruwa Nafisat Abdullahi tana ratuwar jin dadi da kece-raini inda a yanzu haka take tuka tsadaddiyar motar ta kirar Chevrolet Equinox LS ta 2019 mai darajar sama da Naira miliyan 30."

Asali: Legit.ng

Online view pixel