Kannywood: Rayuwata Na Cikin Hatsari, Hadiza Gabon Ta Faɗa Wa Kotu

Kannywood: Rayuwata Na Cikin Hatsari, Hadiza Gabon Ta Faɗa Wa Kotu

  • Jaruma Hadiza Gabon, ta shaida wa Kotun Shari'ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin haɗari duba da rashin tsaro
  • An gurfanar da Hadiza Gabon a gaban Kotun ne bisa zargin ta ƙi auren Bala Musa bayan ya kashe mata N396,000
  • A zaman ɗaya ga watan Agusta, Lauyan Gabon ya roki Kotun ta ɗauke mata zuwa zama saboda rashin tsaro

Kaduna - Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta faɗa wa Kotun shari'ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin haɗari.

Daily Trust ta rahoto cewa wani Bala Musa ya kai ƙarar Jarumar ne bisa zargin ta ƙi aurensa bayan kashe mata kuɗi N396,000.

A baya Gabon ta musanta cewa bata san mutumin ba. Alƙalin Kotun ya ɗage zaman daga 28 ga watan Yuni, 2022 zuwa 1 ga watan Agusta saboda rashin lafiyar matarsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Yi Garkuwa Da Wasu Shararrun Jaruman Fina-Finai A Najeriya

Jaruma Hadiza Gabon.
Kannywood: Rayuwata Na Cikin Hatsari, Hadiza Gabon Ta Faɗa Wa Kotu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Da take jawabi a harabar Kotun, wacce ake zargin ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, ya ce duba da halin rashin tsaron ƙasar nan, Jarumar na jin tsoro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, suna shiga damuwa kowace ranar da Kotu zata yi zaman sauraron shari'ar saboda jarumar na fama da tsegumi a wajen Kotu.

Lauyan ya ce:

"Tsaro na abun dubawa ne, tsaaron jarumar yana da amfani haka kowa da ke cikin Kotun nan har wanda ya kawo ƙarar. Rayuwata na cikin haɗari, rayuwarta na cikin haɗari, haka ta wanda ke ƙara."
"Bamu san wanda ke bibiyar shari'ar a kafafen sada zumunta ba. Nan gaba zaka iya ganin mutane da bindigu sun zo nan sace mutane, wannan shi ne abun da ya dame mu ba wai shari'ar ba."

Lauyan ya roƙi Kotu ta duba tsaron wacce yake wa aiki ta amince a cigaba da shari'ar ba tare da tana halarta ba.

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro Ta Kai Yan Najeriya Bango, NSA Ya Magantu Bayan Taron Yau Da Buhari

Bangaren masu ƙara ba su yarda ba

Da yake martani, Lauyan mai ƙara, Barista Naira Murtala, ya yi watsi da uzurin Gabon na rashin zuwanta zaman Kotu, inda ya ce dole wacce ake ƙara ta halarci zama.

Game da tsaron mai ƙara da wanda ake ƙara, Ya ce ba zai yi musu kan buƙatar ba saboda ƙasar ba tsaro, amma yana buƙatar yin nazari a kai.

Alkalin Kotun, Mai Shari'a Khadi Rilwanu Kyaudai ya tabbatar musu da cewa Kotu zata duba tsaron kowane ɓangare a zama na gaba.

A wani labarin kuma Yan Banga Sun Halaka Wani Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani A Kano

Yan Banga sun halaka wani Malamin makarantar haddar Alƙur'ani da ake kira Tsangaya a Dabai, ƙaramar hukumar Gwale jihar Kano.

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun hau mutumin da duka ba tare da bincike ba bayan ya tsinci wani jariri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel