Yan Bijilanti Sun Halaka Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani a Kano

Yan Bijilanti Sun Halaka Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani a Kano

  • Yan Banga sun halaka wani Malamin makarantar haddar Alƙur'ani da ake kira Tsangaya a Dabai, ƙaramar hukumar Gwale jihar Kano
  • Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron sun hau mutumin da duka ba tare da bincike ba bayan ya tsinci wani jariri
  • Ɗan marigayin ya bayyana cewa yan sanda sun kama Kwamandan Yan Bangan da zargin aikata babban laifi

Kano - Mambobin ƙungiyar yan Banga a garin Dabai, wani yankin ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, sun halaka wani Malami mai koyar da Alƙur'ani.

Bayanai sun nuna cewa an azabtar da Malamin da dukan kawo wuƙa a Ofishin yan Bangan bayan wata mata da ba'a san komai game da ita ba ta zarge shi da sace mata ɗa.

Taswirar jihar Kano.
Yan Bijilanti Sun Halaka Malamin Makarantar Haddar Alkur'ani a Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗan marigayi Malamin mai suna Ibrahim, ya shaida wa jaridar Premium Times ranar Litinin da safe cewa an damƙe kwamandan Yan Banga bisa zargin aikata babban laifi.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kusa Da Wata Babbar Jami'a Najeriya

Ibrahim ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya zo wucewa ta wani wuri sai ya jiyo kukan wani jariri a bola. Ya yanke Shawarin ɗakko shi, garin haka wata mata ta kwalla ihu, tana kiran shi da ɓarawon jarirai."
"Ihun matar ya jawo hankalin yan banga da sauran mazauna yankin, waɗan da suka fara dukansa tun anan. Suka tafi da shi Ofishin Yan Banga suka cigaba da dukansa, ana haka ne ya yanke jiki ya faɗi."
"Wasu mazauna yankin suka gane waye kuma suka gaggauta kai shi Asibiti, amma rai ya yi halinsa tun a kan hanya. Yan Sanda sun kama Kwamandan Yan Banga mai suna Munkaila, ana bincikarsa a Caji Ofis ɗin Rijiyar Zaki."

Ya Aka yi da jaririn?

Ya ƙara da cewa jaririn da aka tsinta an miƙa shi hannun magajin garin kuma yanzun lamarin ya koma hannun yan sanda, "Muna fatan zasu yi wa kowa adalci."

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kashe Kwamandan Jami'an Tsaro A Jihar Arewa

Ba'a samu mai magana da yawun hukumar yan Sanda reshen Kano, Abdullahi Kiyawa, ba lokacin da aka neme shi ta wayar salula domin jin ta bakin hukumar su.

A wani labarin kuma Gwamnatin Katsin ata shirya taro na musamman domin nema wa ƙasa zaman lafiya

Gwamnatin Jihar Ƙatsina ta shirya taron Addu'a na musamman a dukkan sassan jihar don neman Allah ya kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Gwamna Masari, yayin jawabi a wurin taron, ya gode wa Malaman da suka halarci wurin don ba da gudummuwarsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel