Ta tabbata, Jaruma Fati Washa ta maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi a shirin Labarina

Ta tabbata, Jaruma Fati Washa ta maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi a shirin Labarina

  • Fitacciyar jaruma Fati Abdullahi wacce aka fi sani da Fati Washa ta maye gurbin jaruma Nafisa Abdullahi a shiri mai dogon zango na Labarina
  • Kamar yadda bidiyon wurin daukar shirin wanda Darakta Aminu Saira da Fati Washan suka wallafa ya nuna, ana cigaba da daukan shirin da Washan
  • A shekarar da ta gabata ne aka dinga hasashen cewa Fati Washa zata maye gurbin Laila wacce tayi aure, ashe tun a lokacin akwai matsala tsakanin Nafisa da Saira

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ta tabbata cewa jaruma Fatima Abdullahi wacce aka fi sani da Fati Washa ce zata maye gurbin jaruma Nafisa Abdullahi a cikin shiri mai dogon zango na labarina wanda kamfanin Saira Movies ke haskawa.

An gano hakan ne bayan ganin ta da aka yi a wurin daukar shirin zango na biyar a wani gajeren bidiyo wanda Malam Aminu Saira ya wallafa kuma Farti Washan ta sake wallafawa a shafinta na Instagram.

Kara karanta wannan

Kano: Jaruma Raliya ta shirin dadin kowa za ta yi aure, hotuna da katin biki sun fito

Fati Washa
Ta tabbata, Jaruma Fati Washa ta maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi a shirin Labarina. Hoto daga @washafati
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun kafin a san matsalar dake tsakanin Malam Aminu Saira da Jaruma Nafisa Abdullahi, a watan Disamban shekarar da ta gabata ne ya fito ya wallafa hoton Fati Washan inda yake tambayar rawar da ya dace ta taka a shirin.

"Fati Abdullahi, Fati Washa, idan ta bayyana a shirin Labarina Series, wanne gurbi kuke tsammanin za ta maye?" ya wallafa.

Jama'a masu tarin yawa sun yi hasashen cewa za ta maye gurbin Laila ne wacce tayi aure, sai dai kuma gane cewa da aka yi akwai matsala tsakanin jarumar da Aminu Saira ne yasa aka gane cewa Fati Washa ba gurbin Laila zata maye ba.

Ganinta a bidiyon yadda ake daukar shirin ya sake tabbatarwa da jama'a hakan.

An so fara sakin shirin mai dogon zango a watan Yulin nan da muke ciki, sai dai an samu tangarda inda wasu daga cikin jaruman ke fama da rashin lafiya wanda har darakta Aminu Siara ya fito ya bada hakuri tare da bayyana uzirin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari zai kashe wa 'yan Najeriya N6.72trn a matsayin tallafin man fetur

Jaruma Nafisa Abdullahi ta sanar da ficewa daga fim din Labarina, ta sanar da dalilanta

A wani labari na daban da Legit.ng ta kawo muku, an ji cewa, fitacciyar jarumar Kannywood kuma tauraruwar shiri mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi, ta sanar da ficewarta gaba daya daga shirin fim din.

Tun farko, an yi makonni ba a ga jarumar ta bayyana cikin shirin ba sakamakon yadda wasan ya zo na cewa an yi garkuwa da ita, lamarin da yasa masoyanta suka dinga guna-gunin rashin bayyanarta.

Sai dai a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara, jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa takarda a shafin ta na Instagram inda ta sanar da cewa ta fice daga shirin sakamakon tarin ayyukanta da karatu da ya sha mata kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel