Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

Jarumai 5 da ke jan zarensu a masana'antun Kannywood da Nollywood cike da kwarewa

Babban abun birgewa game da Najeriya shi ne kabilu daban-daban da yadda kowa ke kokarin ganin ya zauna lafiya. Hakan bai sha bamban da masana'antar shirya fina-finai ba, domin bangaren wasan kwaikwayo yana da masana'antu da dama.

Wadanda suka yi fice a cikin su a Najeriya sune Kannywood da Nollywood. Duk da dukkan bangarorin na da tazara mai nisan gaske, kuma suna da 'yan kallon da suka sha bamban, akwai wasu jarumai dake aiki tukuru don ganin sun rufe wannan gibin. Ga wasu jarumai da ke kokarin rufe gibi dake tsakanin Kannywood da Nollywood.

Kannywood da Nollywood: Jarumai 5 da ke taka rawar gani a masana’antun fim 2 na kasar nan
Kannywood da Nollywood: Jarumai 5 da ke taka rawar gani a masana’antun fim 2 na kasar nan. Hoto daga @rahamasadau, @sanidanja, @realalinuhu
Asali: Instagram

Ali Nuhu

Wanda aka haifa a 15 ga watan Maris, 1974, ko shakka babu yana daya daga cikin wadanda suka fi kowa suna a masana'antar shirya fina-finan Hausa.

Daga cikin nasarorin sa, an haska shi a sama da fina-finan Hausa 160 da na turanci 110, kuma ya samu lambobin yabo masu tarin yawa. A koda yaushe ana kallon Ali a daya daga cikin manya, kuma jarumai masu fadi a ji a tarihin masana'antar shirya fina-finan Hausa.

Kara karanta wannan

Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

An haife shi a Maiduguri a jihar Borno, amma ya tashi a Jos da Kano. Domin gogewa da kwarewa a sana'ar tasa, yayi jami'ar Kudancin California, inda ya karanta film Production and Cinematic arts.

Ali ya yi fice a sana'arsa ta wasan kwaikwayo a shekarar 1999 a fim din 'Abin sirri ne'. An fi sanin shi saboda rawar da ya taka a Sangaya, wanda shine daya daga cikin manyan fina-finan Hausa da suka yi tashe a lokacin.

Yayin tsallakawa zuwa Nollywood, tauraron fina-finan ya haska a manya shirye-shirye irin su Banana Islam Ghost, Diamond In the Sky (a Netflix production), Zero Hour, da dai sauransu.

Rahama Sadau

Ba dole wasu su sani ba, amma mai nishadantarwa ta fanni daban-daban, Rahama Sadau, tana hadawa da waka da rawa.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa

An haifeta a 7 ga watan Disamba, 1997, ta kuma taso ne a Kaduna. Gogaggiyar jarumar ta shiga gasar rawa a lokacin da tana karama da kuma lokacin da tana makaranta. Tayi suna ne a karshen shekarar 2013 bayan ta shigo masana'antar shirya fina-finan Kannywood da fim dinta a farko, 'Gani ga Wane'.

An tattaro yadda ta shiga masana'antar shirya fina-finan Kannywood a 2013 ta Ali Nuhu. Zuwa 2016, an nadata a matsayin 'Fuskar Kannywood'.

A watan Oktoba 2016, Sadau tayi nasarar tsallakawa zuwa Nollywood, inda aka haska ta a fina-finai masu dogon zango a EbonyiLife TV.

Wasu ayyuka da ta haska a fina-finan Nollywood sun hada da; Up North, Zero Hour, MTV Shuga, Sons of the Caliphate, da dai sauransu.

Sani Danja

Zakakurin jarumin bai tsaya a tsallakawa daga Kannywood zuwa Nollywood kadai ba, sai da ya kara da zama jakadan babban Kamfanin sadarwa na Globacom.

An haifa Sani Musa Abdullahi a 20 ga watan Afirilu, 1973. Etsu Nupe, Yahaya Abubakar, ya nada mawakin kuma dan rawa, a matsayin Zakin Arewa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti

Ya shigo masana'antar shirya fina-finan Hausa a shekarar 1999 a fim 'Dalibai'. Haka zalika, Danja ya samar gami da bada umarni a fina-finai irinsu; Manakisa, Kwarya tabi Kwarya, Jaheed, Nagari, Wasiyya, Harsashi, Gidauniya, Daham, Jarida, Matashiya, da dai sauransu.

Sai dai, ya yi fice a Nollywood a shekarar 2012 a fim mai taken 'Daughter of the River'. Tun lokacin, ya haska a manyan fina-finai irinsu; Nimbe, Gold Statue, Dark Closet, da sauransu.

Paul Sambo

An haife shi a 27 ga watan Janairu, 1976, Paul Sambo jarumi ne kuma mai shirya fina-finai wanda ya haska a fina-finan Kannywood da Nollywood.

A shekarar 2012, ya haska a Mr Brown a wani wasan kwaikwayo mai cike da soyayya mai taken Mr. and Mrs, inda tauraruwarsa ta haska tare da Joseph Benjamin, Paul Apel, Nse Ikpe-Etim, da goggiyar jaruma, Barbara Soki.

Sani Mu'azu

An haife shi a 2 ga watan Mayu, 1960, a Jos, mahaifin 'ya'ya ukun yayi Nigerian Institute of Jounalism a jihar Legas, bayan ya gama University of Jos, inda ya karanta Mass Communication.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Jarumin kuma mai shirya fina-finan yana amsar lambobin yabo, sannan yana daya daga cikin fuskoki masu haskawa a Kannywood.

Sani Mu'azu ya kwashe shekaru kusan ashirin a masana'antar shirya fina-finan Najeriya. Ya samar da wani fim a shekarar 2007 mai taken 'Mountain Blues', wanda ya samu lambar yabo a matsayin fim din da yafi kowanne haduwa a Abuja International Film Festival (AIFF) a shekarar 2919.

Ya yi fice ne a rawar da ya taka a matsayin Sifeta Shehu a gagarumin wasan kwaikwayo, King Of Boys. Haka zalika, ya haska a sauran fina-finan da suka samu lambobin yabo irin su; Lion Heart, Up North, MTV Shuga, da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel