Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa

Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa

  • Janar Buba Mohammed Marwa (murabus), shugaban hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA, ya bayyana cewa an masa tiyata a baya
  • Buba Marwa ya ce an masa tiyatan ne sakamakon wasanni da motsa jiki da ya yi a lokacin yana da kuruciya a rundunar soja
  • Shugaban na NDLEA, yayin zanta wa da manema labarai a hedkwatar hukumar a Abuja ya ce a halin yanzu ya koma bakin aiki gadan-gadan

Abuja - Shugaban hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA, Janar Buba Mohammed Marwa (murabus) ya ce an masa tiyata ne saboda ciwon baya da ke damunsa sakamakon wasanni da ya yi a lokacin yana matashin soja.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin amsa tambayoyi da manema labarai bayan taron da ya yi da wasu kwararru a bangaren rage safarar kwayoyi a ofishinsa da ke hedkwatar NDLEA a Abuja, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Sheikh Zakzaky: Ina burin komawa Zariya na ci gaba da abin da nake yi a baya

Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa
Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Buba Marwa. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Da aka tambaye shi idan an kwantar da shi a asibitin Landan domin yi masa tiyata kamar yadda jita-jita ke cewa, Marwa ya ce:

"Eh, a baya-bayan nan an min tiyata saboda ciwon baya sakamakon wasanni da na yi lokacin ina matashin soja. Bayan buga wasan Polo, ina cikin tawagar masu gudu a rundunar sojoji a 1970s kuma na yi tsallen long jump da hockey."

Ya kara da cewa tuni ya koma bakin aikinsa domin karfafa hukumar wurin yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.

Tunda farko, a wurin taron, jagoran tawagar kuma direkan, Smiths Detection, reshen Africa, Mr Gabriel Pequignot ya ce an yi taron ne domin tattaunawa kan hadin gwiwa.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel