Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa

Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa

  • Bayyanar tsohuwar budurwar ango Furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wato Maryam Yahaya a wurin bikinsa ya bai wa jama'a mamaki
  • Tun bayan fara shirin bikin, jaruma Maryam Yahaya bata wallafa kati ko hotunan kafin aure na tsohon saurayinta ba, lamarin da yasa aka dinga cewa kishi ta ke
  • Ko da ta halarci bikin, an hango Maryam Yahaya tana baya-baya ba tare da ta zake ba wurin bikin, sai dai kuma ta dauka wanka iya wanka

A yayin shagalin bikin Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da Hassana Muhammad, jarumai, mawaka da dukkan 'yan masana'antar sun samu halarta, hakan yasa aka yi bikin a fili domin dakin taro ba dole ya dauke su ba.

'Yan fim abokan sana'arsu sun matukar yi musu kara inda suka fito kwan su da kwarkwatarsu suka halarci bikin.

Manya irinsu Ali Nuhu, Rarara, Adam Zango duk sun halarta, kai hatta manyan mata irinsu Saratu Gidado, Hadizan Saima, Teema Makamashi duk sun samu halartar wurin bikin.

Kara karanta wannan

Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa
Zafafan hotunan wankan da Maryam Yahaya, tsohuwar budurwar Maishadda ta dauka a wurin bikinsa. Hoto daga @real_maryamyahaya
Asali: Instagram

Wannan kuwa ba ya rasa alaka da ganin cewa a lokaci mai tsawo ne da dan masana'antar ya aura 'yar masana'antar, za mu iya cewa tuwo na mai na ne bikin.

Sai dai duk wannan ba shi ya fi daukar hankali ba kamar irin ganin tsohuwar budurwar angon, wato Maryam Yahaya a wurin bikin, wacce ba a taba tsammanin za ta halarci bikin ba saboda wasu dalilai.

Tun bayan fara shirin bikin ake ta kananan maganganu kan yadda Maryam Yahaya ba ta wallafa katin bikin ko hotunan kafin auren tsohon saurayin nata ba duk da ana ta taya su murna.

Jama'a da dama sun alakanta hakan da kishi ganin cewa tsohon saurayinta ne.

Kwatsam kuwa sai ga Maryam a wurin shagalin bikin cikin murna da farin cikinta har da dinka ankon biki ta saka, sai dai bata zake ba ta dinga komai baya-baya.

Kara karanta wannan

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

Ga wasu daga cikin hotunan wankan da ta dauka a wurin bikin:

Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana

A wani labari na daban, kyawawan hotunan furosuda Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad sun bayyana ana sauran kwanaki kalilan bikin masoyan.

Tun dai a karshen watan Fabrairu aka bayyana cewa furodusa Maishadda zai angwance da maasoyiyarsa Hassana Muhammad kuma katin bikin ya karade kafafen sada zumunta ta Instagram.

A safiyar yau Laraba ne jaruma Hassana Muhammad ta wallafa kyawawan hotunanta tare da angonta wanda suka sha kyau ba kadan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel