Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana

Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana

  • Jaruma Hassana Muhammad ta wallafa kyawawan hotunanta tare da masoyinta Abubakar Bashir Maishadda
  • Hotunan dai na kafin auren masoyan sun bayyana ne ana sauran kwanaki uku a daura aurensu a jihar Gombe
  • Tuni masoya, 'yan uwa da abokan arzikin jaruma Hassana Muhammad da Furodusa Maishadda suka dinga yi musu murna

Kyawawan hotunan furosuda Abubakar Bashir Maishadda tare da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad sun bayyana ana sauran kwanaki kalilan bikin masoyan.

Tun dai a karshen watan Fabrairu aka bayyana cewa furodusa Maishadda zai angwance da maasoyiyarsa Hassana Muhammad kuma katin bikin ya karade kafafen sada zumunta ta Instagram.

Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana
Zafafan Hotunan kafin aure na jaruma Hassana Muh'd da Furodusa Maishadda sun bayyana. Hoto daga @realhassana_muhd
Asali: Instagram

A safiyar yau Laraba ne jaruma Hassana Muhammad ta wallafa kyawawan hotunanta tare da angonta wanda suka sha kyau ba kadan ba.

Kara karanta wannan

Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari

Jama'a da dama sun dinga taya su murnar wannan abun farin ciki da zai same su cikin kwanaki kadan masu zuwa, inda masoyansu suke cigaba da yi musu Allah sam barka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel