Akwai sabon shagali tafe: Jarumar Kannywood, Teema Yola za ta shiga daga ciki

Akwai sabon shagali tafe: Jarumar Kannywood, Teema Yola za ta shiga daga ciki

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola na shirin raya sunnah
  • A yan baya-bayan nan dai jaruman masana'antar shirya fina-finan na Hausa na ta yin aure lamarin da ya baiwa mutane da dama mamaki
  • Jaruma Umma Shehu ce ta sanar da labarin shirye-shiryen auren abokiyar sana'ar tata

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa wacce tauraronta ke kan haskawa, Fatima Isa da akafi sani da Teema Yola na shirin shiga daga ciki.

A cikin yan watannin nan ana ta shan shagalin bukukuwa a masana’antar ta kannywood, inda zuwa yanzu aka daura auren akalla jarumai hudu da furodusa daya.

An fara ne da auren jarumai mata biyu a karshen watan Fabrairu wato Hafsat Idris Barauniya da Aisha Aliyu tsamiya, sai kuma na jaruma Hassana Moh’d wacce ta auri babban furodusan masana’antar, Abubakar Bashir Maishadda a ranar 13 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

Akwai sabon shagali tafe: Jarumar Kannywood, Teema Yola za ta shiga daga ciki
Akwai sabon shagali tafe: Jarumar Kannywood, Teema Yola za ta shiga daga ciki Hoto: teema_yola /official_ummahshehu
Asali: Instagram

A yanzu kuma mun samu labarin shirye-shiryen auren Jaruma Teema Yola wanda abokiyar sana’arta, Umma Shehu ta sanar a shafinta na Instagram.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Koda dai Umma shehu bata bayyana ranar da za a daura auren Teema ba, ta tabbatar da cewar ita ce ta gaba a kan layi. Ta kuma wallafa bidiyon jarumar tare da wanda ke shirin zama angon nata.

Umma ta rubuta a shafinta:

“Ma’auratanmu nan gaba Insha Allah.”

Jama'a da dama sun tofa albarkacin bakunansu tare da taya jarumar murna

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi bayan samun labarin shirin auren jarumar.

official_hafsaidris20 ta yi martani:

"Masha Allah "

mis_yabour ta ce:

"Allah yakaimu,gaskiya haka yafi ban tabajin yan Hausa film sun burgeniba sai bana"

ummirahaboficial ta ce:

"Masha Allah ❤️❤️❤️"

muhammadsamira034 ya ce:

Kara karanta wannan

Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana

"Masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi"

priyankapinky533 ta ce:

"Toh fa yan Kennywood sai kace Wanda aka muku gorin Aure anyway Masha Allah an fara hankali"

Alkawarin Allah ya cika: Aure ya dauru tsakanin Furodusa Maishadda da jaruma Hassana

A ranar Lahadi, 13 ga watan Maris ne dubban jama’a suka shaida daurin aure tsakanin babban furodusan masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da jarumar fim, Hassana Mohammed.

Auren wanda aka daura a Masallacin Murtala da ke birnin Kano, ya samu halartan manyan jaruman masana’antar wadanda suka nuna kara sosai ga abokan sana’ar tasu.

Tun farko dai labarin auren ya ja hankalin jama'a duba ga yadda ba'a cika aure tsakanin yan fim ba, domin sun fi auren yan waje, illa yan tsiraru da suka kulla auratayya a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel