Maryam Booth: Bana jin shakkar gayawa mahaifiyata duk abun da nake ciki na rayuwa, koda laifi na aikata

Maryam Booth: Bana jin shakkar gayawa mahaifiyata duk abun da nake ciki na rayuwa, koda laifi na aikata

  • Jarumar Kannywood, Maryam Booth ta bayyana cewa har yanzu bata samu babbar kawar da za ta maye mata gurbin mahaifiyarta ba
  • Maryam ta bayyana cewa akwai shakuwa tsakaninta da mahaifiyarta ta yadda bata iya boye mata komai da take ciki a rayuwa
  • Ta ce koda laifi ta aikata, za ta iya samun mahaifiyar tata kai tsaye ta fada mata, koda kuwa za ta yi mata fada sai ta fara sauraronta

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Adam Booth wacce aka fi sani da Dijangala ta yi wasu zantuka masu ratsa zuciya game da mahaifiyarta, Marigayiya Zainab Booth.

Jarumar, ta bayyana cewa har yanzu bata samu wanda zai maye mata gurbin mahaifiyarta ba da sunan babbar kawa, domin a cewarta mahaifiyarta ce babbar kawarta wacce bata jin shakkar gayawa sirrinta a rayuwa.

Kara karanta wannan

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

Maryam Booth: Bana jin shakkar gayawa mahaifiyata duk abun da nake ciki na rayuwa, koda laifi na aikata
Maryam Booth: Bana jin shakkar gayawa mahaifiyata duk abun da nake ciki na rayuwa, koda laifi na aikata Hoto: Fim Magazine
Asali: UGC

Ta ce koda kuwa laifi ta aikata, tana iya samun mahaifiyar tata ta gaya mata kai tsaye, cewa koda za ta yi mata fada, za dai ta tsaya ta saurareta.

Maryam ta fadi hakan ne a yayin wata hira da sashin BBC na Hausa a shirin nan na ‘Daga bakin mai ita’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambayi jarumar cewa wacece babbar kawarki, sai ta ce:

"Har yanzu ban samu babbar kawar da za ta maye mun gurbin mahaifiyata ba saboda mamana ita ce babbar kawata, ita ce wacce babu abun da nake boye mata. Duk abun da na yi ko mai laifi ne zan iya samun mamana in gaya mata, koda za ta yi mun fada, za dai ta tsaya ta saurare ni.
"Kuma ita ce wacce bana jin tsoro, bana shakkar gaya mata duk abun da nake ciki na rayuwa, saboda za ta fito ta ce mun gashi-gashi kema kin yi laifi, kazakaza. Toh har yanzu ban samu wacce za ta maye mun gurbin ba. Babu."

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

BBC ta tambayi jarumar game da wanda ya fi birgeta a masana’antarsu ta Kannywood, sai ta ce Marigayi Rabilu Musa Ibro ne ya fi birge ta inda ta ce har yanzu tana kallon fina-finansa.

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

A gefe guda, Maryam Booth ta magantu a kan wasu tambayoyi biyu da mutane ke yawan yi mata wanda a cewarta ta gaji da amsa su.

A wata hira da aka yi da ita a shirin BBC Hausa mai suna ‘Daga bakin mai ita’ jarumar ta ce mutane na yawan yi mata tambayar yaushe za ta yi aure ko kuma menene yasa ta rame.

Asali: Legit.ng

Online view pixel