Batun Ladin Cimma: Jarumin fim ya yi barazanar tona asirin Naziru Sarkin waka, da sauran furodusoshi

Batun Ladin Cimma: Jarumin fim ya yi barazanar tona asirin Naziru Sarkin waka, da sauran furodusoshi

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi ya yi martani ga Naziru Sarkin Waka a kan caccakar da ya yiwa Ali Nuhu da Falalu Dorayi
  • Naziru dai ya ce babu Allah a ran manyan jaruman masana'antar kan cewa da suka yi basu san ana biyan Ladin N2,000 a matsayin kudin aiki ba, inda ya kalubalance su da su yi rantsuwa
  • Abdullahi ya ce sam mawakin bai yiwa jaruman adalci ba inda ya bukace shi da ya karkata wajen yiwa wadanda basa biyan aikin yadda ya kamata wa'azi ciki harda dan uwansa

Furucin da dattijuwar jarumar Kannywood, Ladin Cima ta yi na cewar ba a taba biyanta manyan kudi ba a harkar fim ba hasalima N2,000 zuwa N5,000 ake bata yana ci gaba da tayar da kura a tsakanin manyan jaruman masana'antar.

Kara karanta wannan

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

A yanzu jarumi Nuhu Abdullahi ya fito ya soki mawaki Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka, cewa bai yi adalci ba wajen yiwa Ali Nuhu da Falalu Dorayi kudin goro bayan sun fito sun bayyana su ga abun da suke biyan jarumar.

Da za mu fito mu yi bayani da mutuncinku ya zube - Nuhu Abdullahi ga Naziru sarkin waka
Da za mu fito mu yi bayani da mutuncinku ya zube - Nuhu Abdullahi ga Naziru sarkin waka Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram, Abdullahi ya bayyana cewa da ace za su fito suyi magana da mutuncin su Naziru sai ya zube.

Ya kuma shawarci mawakin da ya karkata wajen yiwa marasa biyan aiki daidai wa'azi ciki kuwa harda da dan uwansa wanda yace baya biya yadda ya kamata.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Jan hankali; Akwai bukatar duk lokacin da mutum zai yi magana ya yi adalci, Falalu Dorayi da Ali Nuhu sun ce ga yadda suke biyan Mama Tambaya kudin aiki, BBC Hausa ta tabbatar da hakan wurin ta.

Kara karanta wannan

Abun alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara, ya taba zukatan jama'a

"Naziru kafito ka yi kudin Goro baka kyauta ba. Sai ka yi musu adalci da ire-iren su da su ke biyan hakkin aiki yadda Yakamata.
"Wadanda kuma basa biyan hakkin mutane idan anyi mu su aiki harda “Dan’uwan ka” yana ciki sai kacigaba da yi mu su wa’azi, Allah ya shirye su!"

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

A gefe guda, mun kawo a baya cewa shahararren mawakin nan kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka ya yi martani a kan lamarin Ladin Cima.

Tun farko dai dattijuwar jarumar ta bayyana a wata hira da BBC Hausa cewa a kan bata N2,000 zuwa N5,000 ne idan ta fito a shirin fim.

Sai dai wasu manyan daraktoci irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi sun fito sun musanta haka, inda kowannensu ya ce ya bata N40,000 a fina-finan da tayi masu.

Kara karanta wannan

Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel