Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo

  • Mawakin Kannywood Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka ya yi martani a kan lamarin Ladin Cima
  • Sarkin waka ya bukaci Ali Nuhu da Falalu A Dorayi da su ji tsoron Allah kan cewa basu san ana biyan N2,000 ba a harkar fim
  • Naziru ya ce tabbass har N1,000 ana biya domin wani ma sai dai jarumi ya biya ko jaruma ta bayar da kanta ayi lalata da ita kafin a saka ta a wasu fina-finan

Shahararren mawakin nan kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka ya yi martani a kan lamarin Ladin Cima.

Tun farko dai dattijuwar jarumar ta bayyana a wata hira da BBC Hausa cewa a kan bata N2,000 zuwa N5,000 ne idan ta fito a shirin fim.

Kara karanta wannan

Kannywood: Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tada hazo a masana'antar

Sai dai wasu manyan daraktoci irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi sun fito sun musanta haka, inda kowannensu ya ce ya bata N40,000 a fina-finan da tayi masu.

Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo
Ladin Cima: Naziru sarkin waka ya yiwa Ali Nuhu da Falalu wankin babban bargo Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

A martaninsa, Naziru ya kalubanci yan fim din da suka karyata tsohuwar da su ji tsoron Allah, harma ya ce sam babu Allah a zuciyarsu.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Naziru ya ce karya ne Falalu da Ali su ce basu san ana baiwa tsoffi kudi kamar N2,000 ba.

Naziru ya ce:

“Assalamu alaikum Jama’a, barkanmu da dare. Wato ayi hakuri kamar shi ba bacin rai ba, bacin rai haka yake. Wannan maganar ta Ladi ni yanzun nan na hadu da ita a soshiyal midiya, gaskiyar magana yan fim ba Allah a ranku, babu.

Kara karanta wannan

Ni nan na bata N40k a fim din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cima

“Kwata-kwata wadanda suka yi magana, suka karyata maganar da matar nan tayi wallahi babu Allah a ranku. Yanzu kamar wadanda naga maganganinsu, mutum biyu Ali Nuhu da Falalu Dorayi dan Allah don Annabi kune za ku ce baku san ana yiwa dattijan nan wannan abun ba? Su tashi aiki a dau N2,000 ko N1,000 ko ace masu su tafi za a kira su, haba ku ji tsoron Allah, mu ji tsoron Allah mana.
“Matar nan yanzu mu fara daga kan Falalu A Dorayi, matar nan a kirga fim nawa tayi a industiri, fim nawa ne ka saka ta? Har za ka karyata maganarta don ta ce N2,000 ko N4,000 ake bata. Ya kamata ace idan tayi fim 20 sai aka biyata wannan kudin a 18 shine idan tayi maganar bata yi daidai ba. Amma idan ta yi 20 Falalu fim nawa ne aka sa ta?
“Darakta mu yi maganar gaskiya mana, da mu da ku mun san cewa yaran nan za ka sa mutum a matsayin furodusa amma ya zo yana cutar mutane. Ba ma kokari mu biyasu da kanmu mun san da wannan.

Kara karanta wannan

Abun alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara, ya taba zukatan jama'a

“Ko kuma shi Ali Nuhu fim nawa ya sa ta? Nawa ne ya biyata N40,000? Mun sani ba karya bane ba. Kwanaki an yi wannan na kira mutane su zo suyi fim tsofaffi ne na kira su, ina tambaya nawa ake biyansu aka ce N2,000. Mun san wannan maganar ku bar tsohuwa ta huta lafiya. Wannan da gaske ne ba ita kadai bace ba, ba kuma tsofaffi kawai ake ma haka ba.
“Duk wanda za a sa a fim idan dai zai fito sau daya, biyu ko uku ne sai dai a basu irin wannan kudin, shiyasa harkar take ta yin kasa, kawai idan za ku gyara, ku gyara, ku dunga biyan mutane da kanku.
“Yanzu so kuke yi tunani ya kama wannan tsohuwar ko wani ciwo ya zo ya kamata, ni na rantse haka ake biya a wannan harka amma idan wani ya isa ya fito ya rantse cewa bah aka ake yi ba.”

Kara karanta wannan

Wanda ICPC ta ke zargi da laifin satar Naira miliyan 900 yana so ayi sulhu a wajen kotu

Ni nan na bata N40k a fim din Gidan Badamasi, Furodusan Kannywood ya yi martani ga batun Ladin Cimma

A baya mun ji cewa fitaccen furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nazir Adam Salihi, ya magantu a kan ikirarin da Jaruma Ladin Cima ta yi na cewa ba a taba biyanta kudi masu tsoka a harkar fim ba.

Salihi wanda ya yi martani ga ikirarin da dattijuwar jarumar ta yi na cewar ba a taba biyanta N50,000 ko N30,000 ko N20,000 ba fim hasalima fitowa ta karshe da tayi N2,000 aka bata, ya ce babu gaskiya a cikin zancenta.

Furodusan ya ce shi kanshi ya bata N40,000 a cikin fim din Gidan Badamasi mai dogon zango kashi na uku, sannan kuma cewa ya sake bata N30,000 a kashi na hudu, jaridar Aminiya ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel