Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab

Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab

  • Jarumi kuma mawakin Kannywood, Lilin Baba ya taya masoyiyarsa Jaruma Ummi Rahab murnar zagayowar ranar haihuwarta
  • Lilin Baba ya je shafinsa na soshiyal midiya domin yin kalaman soyayya ga burin zuciyar tasa
  • Ya kuma bayyana cewar ya kusa yin wuff da ita idan har Allah ya yarda

Soyayya dai na kara karfi a tsakanin jaruman Kannywood masu tasowa wato Shu’aibu Ahmed Abbas wanda aka fi sani da Lilin Baba da Ummi Rahab.

Ga dukkan alamu dai soyayyar tasu za ta kai su ga shiga daga ciki nan ba da dadewa ba. Hasashen hakan ya biyo bayan wata wallafa da jarumin mawakin ya yi a shafinsa na soshiyal midiya.

Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab
Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab Hoto: HausaMini.Com
Asali: UGC

Lilin Baba dai ya je shafinsa na Instagram domin taya masoyiyar tasa murnar zagayowar ranar haihuwarta a yau Laraba, 2 ga watan Fabrairu, inda ya jero zantuka masu ratsa zuciyar masoya.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Har ila yau, sakon taya murnar da ya aike mata, Lilin Baba ya karfafa mata gwiwar cewa in shaa Allah ya kusa ya yi wuff da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa abar kaunar rayuwata @ummirahabofficial. Hakika ke ta daban ce mai zuciyar zinari.
"Ina aika sakon zagayowar ranar haihuwa ta musamman gare ki yayin da kika kara shekara daya a yau! Ina fatan kin cika da farin ciki da annashuwa a yau. Abun farin ciki ne ganin irin matar da kika zama a yau. #HappyBirthday UMMI.
"Ina miki fatan alkhairi a duniya da lahira, Allah ya ci gaba da sanya albarka a rayuwarki. Karin nasara a gare ki . NA KUSA NA YI WUFF DA KE IN SHAA ALLAH."

Jaruma Ummi Rahab ta gargadi Adam Zango, ta yi barazanar tona masa 'asiri'

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

A wani labarin, mun kawo a baya cewa fitacciyar jarumar kannywood Ummi Rahab, wacce ta yi fice saboda Ubangidanta, Adam Zango bayan kacamewar wani rikici tsakaninsu ta magantu.

Kamar yadda mujallar fim ta wallafa, jarumar ta yi wa Zango kashedi inda tace matsawar ya cigaba da yada maganganu na batanci a kanta, za ta fallasa asirinsa.

Barazanar da ta janyo mata zage-zage da munanan kalamai daga masoyan Adam Zango.

Asali: Legit.ng

Online view pixel