Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni

Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni

  • Matar shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta yi kira ga kafafen watsa labarai su rinka bibiyar ayyukan alherin da matan gwamnoni suke yi
  • Aisha Buhari tace matan gwamnonin ƙasar nan suna taimaka wa sosai a rayuwar mata, matasa da ƙananan yara
  • A cewarta ya kamata a samu haɗin kai tsakanin waɗannan ɓangarorin domin watsa ayyukan da matan suke yiwa al'umma

Abuja - Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta yi kira ga manema labarai da su rinka bayyana ɗumbin ayyukan da matan gwamnoni ke yi wa al'umma.

Punch ta rahoto cewa ta yi wannan kiran ne ranar Laraba da daddare, a wurin taron karrama matan, waɗanda suka taka rawa a rayuwar mutane, musamman talakawa.

Aisha, wadda ta kasance bakuwa ta musamman a wurin taron, ta samu wakilcin, Aliyu Abdullahi, mai taimaka mata ta ɓangaren yaɗa labarai da hulɗa da jama'a.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Aisha Buhari
Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni Hoto: @Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Matar shugaban ƙasa tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Naji daɗi da aka gayyace ni wannan taron, wanda aka shirya domin karrama mata bisa kokarin da suke ga al'umma."
"Ina son yin amfani da wannan damar wajen kira da kafafen watsa labarai da su rinka bibiyar matan shugabanni domin watsa ayyukan alherin da suke."
"Haɗin kai tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu nasara ce kan nasara kowa zai samu damar sauke nauyin dake kansa, matan suna yin aiki, manema labarai su watsa."

Aisha ta yaba wa waɗanda suka shirya taron

Matar shuagaban ta yaba wa shugabannin gidan jaridar da suka shirya taron karrama gwarazan matan gwamnonin.

Ta kuma ƙara da cewa wannan zai taka muhimmiyar rawa wajen fito da irin cigaban da matan ke kawo wa a mulkin demokaraɗiyya.

A cewarta matan na kokari sosai wajen gudanar da ayyukan jin kai kuma suna taimakawa wajen kare rayuwar mata, ƙananan yara da matasa.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

A wani labarin kuma Peter Obi ya maida zazzafan martani kan maƙudan kudin da Buhari ya ware wa ofishin matarsa Aisha Buhari

Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi kaca-kaca da kasafinkuɗin da Gwamnatin Buhari ta ware wa Ofishin Aisha.

Obi yace babu ofishin matar shugaban ƙasa a kundin tsarin mulki, kuma akwai ɓangarorin da suka fi nan muhummanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262