An Zo Wajen: An Nemi a Yi wa Trump Gwajin Kwakwalwa kan Yakin Iran

An Zo Wajen: An Nemi a Yi wa Trump Gwajin Kwakwalwa kan Yakin Iran

  • Daya daga cikin 'yan majalisun Amurka, Jamie Raskin, ya mika bukatar yi wa shugaba Donald Trump gwajin kwakwalwa game da lafiyarsa
  • Jamie Raskin ya bayyana cewa akwai bukatar sanin lafiyar shugaba Trump lura da wasu magangu masu karo da juna da ya rika yi kwanan nan
  • Dan majalisar ya sanar da likitan fadar White House cewa ya kamata a mika musu rahoto na musamman bayan kammala yi wa Trump gwaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Dan majalisar Amurka, Jamie Raskin, ya bukaci likitan Fadar White House da ya gudanar da gwajin kwakwalwa ga Shugaba Donald Trump sakamakon kalamansa masu tsauri kan yaƙin Amurka da Iran.

Dan jam’iyyar Democrat daga Maryland ya bi sahun wasu ’yan majalisar da suka nuna damuwa a kwanakin nan kan yadda shugaban ke tafiyar da rikicin da kuma kalamansa a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump ya kama kai yayin jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana neman yi wa Donald Trump gwajin kwakwalwa

CNN ta wallafa cewa 'yan siyasar Amurka, musamman ’yan Democrat sun fara tambayar ko Trump yana da cikakkiyar ƙwarewar da ta dace don ci gaba da shugabancin kasar.

“A cikin kwanakin nan, ƙasar ta ga yadda kalaman Shugaba Trump ke ƙara zama marasa tsari, masu karo da juna, cike da kalamai masu hadari, rudani da kuma barazana,”

In ji Raskin a cikin wata wasiƙa

Raskin ya bayar da dalilai da dama kan shakku game da lafiyar Trump, ciki har da sakon Easter da Trump ya wallafa mai cike da kalamai masu hadari yana kira ga Iran ta buɗe mashigar Hormuz.

Yahoo News ta wallafa cewa ya kuma ambaci furucin Trump na cewa zai shafe Iran a doron kasa idan ba ta amince da sharudansa ba kafin wa’adin da ya saka.

Za a duba lafiyar Shugaba Trump

Ana ganin ba lallai wannan buƙata ta haifar da wani sakamako ba domin Trump yakan yi alfahari da cewa yana cin gwajin kwakwalwa.

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

Baya ga haka, likitan White House ya bayyana shi a matsayin mai cikakkiyar lafiyai a gwajin shekara-shekara da aka masa a bana.

Dan majalisar Amurka, Jamie Raskin
Jamie Raskin da ya nemi a yi wa Donald Trump gwajin kwakwalwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana so a tsige Trump a Amurka

Wasiƙar dan majalisar na zuwa ne a lokacin da wasu daga cikin ’yan Democrat da ma wasu manyan masu goyon bayan MAGA ke ganin ya kamata a cire Trump ta hanyar kundin tsarin mulki ko kuma a tsige shi.

Domin cire Trump daga mulki ta hanyar sashe na 25, dole ne mafi yawan mambobin majalisar ministocinsa tare da mataimakin shugaban ƙasa su amince da hakan.

Sai dai babu wata alama cewa ministocinsa na tunanin hakan, ko kuma mataimakin shugaban ƙasa JD Vance zai goyi bayan hakan.

Trump ya gargadi Netanyahu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya gargadi Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan kai hari kasar Lebanon.

Trump ya yi magana ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke matsawa kan cewa dole a sanya Lebanon a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta.

A daya bangaren, kasar Iran ta yi barazanar kin shiga tattaunawa da Amurka da za a yi bayan tsagaita wuta har sai bayan daina kai hari Lebanon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng