Yemen Ta Shiga Yakin Iran Gadan Gadan, Ta Harba Makami Mai Linzami zuwa Isra'ila

Yemen Ta Shiga Yakin Iran Gadan Gadan, Ta Harba Makami Mai Linzami zuwa Isra'ila

  • Rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga ƙasar Yemen a yau Alhamis
  • Sautin ƙararrawar gargadi ya cika biranen Isra'ila yayin da take ke fuskantar ruwan makamai masu linzami daga Iran, yemen da Lebanon
  • A gefe guda, sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa sun kashe Jamshid Eshaqim, babban kwamandan hedikwatar man fetur na Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila – Tsaro ya ƙara taɓarɓarewa a Gabas ta Tsakiya a yau Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026, bayan da rundunar sojin Isra'ila ta sanar da gano tare da kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo daga ƙasar Yemen.

Wannan shi ne hari na huɗu da dakarun ƴan tawayen Houthi na Yemen suka kai wa Isra'ila tun bayan ɓallewar yaƙin yankin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila

Yemen ta harba makami mai linzami kan Isra'ila.
Wani makami mai linzami da Iran ta harba zuwa cikin Tel Aviv na Isra'ila. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Yemen ta harba makami zuwa Isra'ila

Ƴan Houthi sun tabbatar da cewa sun kai harin ne tare da haɗin gwiwar dakarun Iran da na Hezbollah, a cewar rahoton Aljazeera.

Hukumar kiyaye haɗurra ta Isra'ila ta kunna ƙararrawar gargaɗi a mafi yawancin biranen ƙasar, ciki har da Kudus da yankin Bahar Mayit (Tekun gishiri).

Mazauna waɗannan yankuna sun nemi mafaka na tsawon lokaci har sai da sojoji suka ba da tabbacin cewa an kakkabo makamin kuma ba sa cikin hadari a lokacin.

Iran ma ta harba makamai kan Isra'ila

Baya ga harin na Yemen, Isra'ila ta fuskanci wani gagarumin harin makamai masu linzami daga ƙasar Iran a yau, kamar yadda rahoton IFRC ya nuna.

Hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom ta bayar da rahoton cewa wani mutum ɗan kusan shekara 30 ya ji rauni a baya sakamakon fadowar baraguzan makamin da Iran ta harba.

Kara karanta wannan

Rundunar IRGC ta yi wa Isra'ila barna a sababbin hare haren makami mai linzami

Yayin da jami'an Magen David Adom suke kokarin bada agajin gaggawa a wuraren da aka samun fashewar makamai, an kunna kararrawar gargadi a Yammacin Galilee bayan Isra'ila ta hango tahowar rokoki daga Lebanon.

Yemen, Iran, Lebanon sun yi ruwan makamai kan Isra'ila
An ga hasken fitar rokoki a sararin Tel Aviv a wani kokari na kakkabe makaman da Iran ta harbo. Hoto: JACK GUEZ / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Martanin sojojin Isra'ila

A daidai lokacin da take kakkabo waɗannan makamai, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa ta kashe babban kwamandan hedikwatar man fetur na dakarun Iran, Jamshid Eshaqim, a wani hari da ta kai birnin Tehran.

Isra'ila ta ce wannan hedikwata ita ce take samar da kuɗaɗen da Iran ke amfani da su wajen ƙera makamai da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin dake yaƙar ta, a cewar rahoton The Jerusalem Post.

Wannan gagarumin hari na yau ya haifar da fargabar cewa yaƙin na iya faɗaɗa zuwa dukkan sassan yankin, musamman ganin yadda Iran, Hezbollah da ƴan Houthi suka duƙufa wajen kai wa Isra'ila hare-hare na "ruwan wuta" a lokaci guda.

Iran ta harba makamai 300 lokaci guda

A wani labari, mun ruwaito cewa, Iran ta sanar da harba makamai masu linzami da suka haura 100 tare da rokoki 300 kan sansanonin sojin Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Iran ta yi luguden wuta kan Amurka da Isra'ila, ta farmaki muhimman wurare

Rahotanni sun nuna cewa an lalata jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a sansanin Al-Adiri dake kasar Kuwait yayin harin daren Laraba, 1 ga Afrilu, 2026.

Iran dai ta gargadi ma'aikatan Google, Microsoft dake Gabas ta Tsakiya da su yi ta kansu domin za ta kai hare hare kan kamfanonin Amurka 18.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com