Iran Ta Yi Iƙirarin Kai Harin Bama Bamai a kan Wasu Sansanoni a UAE da Kuwait, Ta Fadi Dalili
- Iran ta tabbatar da cewa ita ce ta kai hare-hare kan sansanonin soji a Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait
- Ƙasar ta bayyana cewa harin ya lalata wasu muhimman wurare da ta aika makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
- Kasashen da abin ya shafa, wato UAE da Kuwait ba su yi martani ba duk da zargin da Iran ta yi a kan sansanonin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Iran – Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ta kai hare-hare kan wasu sansanonin soji a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Kuwait.
Ta bayyana haka ne a lokacin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai mata munanan hare-hare da kashe manyan jami'an gwamnatin kasar.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta wallafa cewa rahotanni daga kasar sun ce rundunar ruwan Iran ce ta kai hare-haren, inda ta yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa wajen kai farmakin.
Iran ta kai hari Kuwait da UAE
Anadolu Ajansi ta ruwaito sanarwar ta ce an lalata wasu muhimman wurare a sansanin Al-Minhad da ke UAE da kuma sansanin jiragen sama na Ali Al Salem da ke Kuwait.
Ta ƙara da cewa hare-haren sun shafi rumfunan ajiye jirage da tankunan mai da ta tabbatar suna da alaƙa da Amurka a yankin.
Kasar ta kuma yi zargin cewa wuraren da aka kai wa harin ana amfani da su ne wajen kai hare-hare kan yankunan Iran.
Sai dai, ba a samu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari na Iran ba zuwa yanzu.
Martanin UAE da Kuwait kan harin Iran
Duk da iƙirarin da Iran ta yi, babu wata ƙasa ko ƙungiya mai zaman kanta da ta tabbatar da faruwar hare-haren ko irin barnar da aka yi.
Har ila yau, hukumomin ƙasashen UAE da Kuwait ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da lamarin, abin da ya ƙara jefa shakku kan sahihancin rahoton.
Masu lura da al’amuran tsaro na ƙasa da ƙasa na cewa irin waɗannan iƙirare na iya ƙara dagula al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda tuni ke fama da tashin hankali.

Source: Twitter
Rahotanni irin wannan na zuwa ne a lokacin da ake samun ƙara tsami tsakanin Iran da wasu ƙasashen yamma, musamman kan batutuwan tsaro da zargin kai hare-hare ta ɓoye.
A halin yanzu, duniya na ci gaba da bibiyar lamarin domin ganin ko za a samu ƙarin bayani daga bangarorin da abin ya shafa, ko kuma wasu hujjoji da za su tabbatar ko ƙaryata wannan iƙirari.
Iran ta kai sababbin hare-hare Gabas ta Tsakiya
A baya, mun wallafa cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta nuna cewa a shirye ta ke domin ci gaba da fafatawa da Amurka da Isra'ila Yayin da yaƙi ke ƙara ƙazanta.
IRGC ta kaddamar da sabon farmaki wanda ya tunkari birane da dama a Isra'ila tare da sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ana shagulgulan Sallah.
Rndunar ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kai hare-haren a kan sansanonin da ke da alaƙa da Amurka.
Asali: Legit.ng

