An 'Gano' Waɗanda Suka Taimaka wa Isra'ila da Amurka har Aka Hallaka Khamenei

An 'Gano' Waɗanda Suka Taimaka wa Isra'ila da Amurka har Aka Hallaka Khamenei

  • Rahotanni sun bayyana yadda hukumar leken asiri ta CIA ya ba da gudunmawa wurin farmaki kan Ayatullah Ali Khamenei
  • Majiyoyi sun ce bayanan sirri sun taimaka wa Amurka da Isra’ila kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a harin Tehran
  • An ce CIA ta dade tana bibiyar Khamenei, inda ta gano taron manyan jami’an tsaro da aka shirya a wani katafaren wuri domin tattauna halin da ake ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Wani rahoto ya bayyana cewa bayanan sirri na CIA sun taimaka wajen jagorantar hare-haren da Amurka da Isra’ila.

Harin da aka kai ya taimaka wurin hallaka jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatullah Ali Khamenei wanda ya jawo jimami a kasar.

Yadda aka yi nasarar kashe Khamenei a harin Isra'ila da Amurka
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Donald Trump da marigayi Ali Khamenei. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Rawar da CIA ta taka a kisan Khamenei

Rahoton jaridar The New York Times ya ce CIA ta gano cewa Ayatollah Ali Khamenei zai halarci wani muhimmin taro da manyan jami’an Iran.

Kara karanta wannan

Khamenei da manyan shugabannin tsaron Iran 4 da suka rasu, ya rasa wasu iyalansa

An ce hukumar leken asirin Amurka ta shafe watanni tana bibiyar motsinsa, inda ta gano taron zai gudana safiyar Asabar a Tehran.

Asali Amurka da Isra’ila sun shirya kai harin da dare, amma sun sauya shirin bayan samun bayanan sirri daga CIA.

An bayyana cewa Amurka ta mika bayanan ga Isra’ila, wadda ta tsara yadda za a kai harin kan shugabannin Iran.

Rahoton ya ce an fara aikin ne da misalin karfe shida na safe a Isra’ila, inda makamai masu linzami suka fada sansanin.

Da misalin karfe 9:40 na safe, makamai masu linzami masu nisa suka lalata wurin taron da ke tsakiyar Tehran wanda ya jawo suka daga kasashe daban-daban.

Ana ci gaba da jimamin rasuwar Ali Khamenei a Iran
Marigayi jagoran addini a Iran, Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Manyan jami'an tsaron Iran da suka rasu

Baya ga kisan Khamenei da aka yi a Tehran, an kashe shugaban rundunar IRGC, Janar Mohammad Pakpour, da mai ba da shawara Ali Shamkhani

Sannan an hallaka Ministan tsaron Iran, Aziz Nasirzadeh da kuma shugaban ma'aikatan sojojin Iran, Janar Abdolrahim Mousavi da wasu daga cikin iyalansa.

Hukumar shari’ar Iran ta tabbatar da mutuwar manyan jami’an, yayin da kasar ta fara daukar matakin ramuwar gayya.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan kisan jagoran addinin Iran, Imam Khamenei

An ruwaito cewa Iran ta kai hare-hare a yankin Gulf, ciki har da Abu Dhabi da kusa da sansanonin sojojin kasar Amurka.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce hare-haren sojin Amurka za su ci gaba muddin ya zama dole domin kare kansu daga barazanar Iran.

Ana jimamin mutuwar Ali Khamenei a Iran

Mun ba ku rahoton cewa dubban mutane sun taru a birnin Tehran suna makokin kisan Ayatollah Ali Khamenei bayan harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila.

Rundunar IRGC ta sha alwashin daukar mummunan ramuwar gayya kan Isra’ila da sansanonin Amurka a yankin Gulf yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a yankin.

Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa duk wata ramuwar gayya za ta jawo hari mafi tsanani da ba a taba gani ba inda ya ce ba zai sassauta masu ba ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.