An Gayyaci Manyan Malaman Musulunci 2 daga Najeriya, Za Su Yi Jawabi a Birtaniya
- Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami da shugaban Izala na Najeriya, Abdullahi Bala Lau za su yi jawabi a Birtaniya
- Manyan malumman guda biyu za su halarci taron shekara-shekara na kungiyar musulmin Najeriya mazauna Birtaniya
- Ana sa ran masana, kwararru da shugabanni za su halarci taron wanda zai gudana gobe Lahadi, 26 ga watan Oktoba, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Manchester, Birtaniya – Kungiyar Musulmin Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun gayyaci manyan malaman sunnah domin su gabatar da jawabi a taron shekara-shekara
Taron kungiyar musulmin mai suna Nigeria Muslim Forum UK (NMFUK) zai gudana ne ranar Lahadi, 26 ga watan Oktoba, 2025 a birnin Manchester na kasar Ingila watau Birtaniya.

Source: Facebook
Isa Pantami zai yi jawabi a Manchester
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, shi ne babban bako mai jawabi a taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron na bana mai taken “Ethical Digital Economy: The Future of Community-Centred Islamic Digital Banking” zai mayar da hankali ne kan dangantakar dake tsakanin fasahar zamani, ɗabi’a, da tsarin kuɗin Musulunci a wannan zamani.
Pantami, babban malamin Sunnah a Najeriya zai yi jawabi a wurin wannan taro da zai gudana gobe Lahadi.
An gayyaci Sheikh Abdullahi Bala Lau
Sauran manyan baki da za su yi jawabi sun haɗa da Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) wacce aka fi sani da Izala.
Haka kuma Mr Raza Ullah, wanda shi ne Shugaba kuma wanda ya kafa Pfida, wani dandali na harkokin kudin halar, ethical finance da ke jan hankalin duniya, zai yi jawabi a wurin.
Taron zai samu halartar manyan masana, shugabanni, da kwararru a fannin fasaha da kuɗi, domin tattauna hanyoyin da za a iya amfani da fasahar zamani wajen gina tsarin kuɗi na Musulunci da ya dace da ka’idojin ɗabi’a da adalci.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NMFUK, Dr Bilyaminu Romo ya fitar kan abubuwan da suka tsara a taron wannan shekara.
Abubuwan da taron NMFUK ya kunsa
Ya bayyana cewa jawabin Farfesa Pantami zai mai da hankali ne kan rawar da kirkire-kirkiren fasaha za su taka wajen faɗaɗa harkokin kuɗi a Musulunci a Najeriya.
A rahoton Guardian, Dr. Bilyaminu ya ce:
“Za mu tattauna yadda ƙa’idojin Musulunci za su iya jagorantar kirkire-kirkire a harkar kuɗin dijital, domin tabbatar da gaskiya, haɗin kai, da rabon alheri ga kowa.”
“Taken taron na wannan shekara yana nuna jajircewarmu wajen gina tsarin tattalin arziki na gaskiya da ɗabi’a wanda zai amfani kowa da kowa.”

Source: Facebook
Pantami ya fadi amfanin fasahar AI
A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya kwantar da hankulan masu fargabar cewa mutane za su iya ra ayyuka saboda zuwa fasahar AI.
Pantami, wanda babban malamin addinin Musulunci ne ya ce maimakon haka fasaha za ta samar da sababbin damarmakin aiki ga waɗanda suka kware a harkar.
Tsohon ministan ya jaddada cewa AI na taka muhimmiyar rawa a ci gaban ilimi da tattalin arziki, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta cigaba idan ta yi watsi da wannan sabuwar fasaha.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


