Kafa Kasar Gaza: Kasashen Afrika 4 da ba Su Goyi bayan Falasdinu ko Isra'ila ba
A makon da ya wuce kasashen duniya suka kada kuri'a kan 'yancin kasar Falasdinawa karkashin majalisar duniya.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza - A makon da ya wuce ne kasashe 193 da suke karkashin majalisar dinkin duniya suka kada kuri'a kan samar da kasa wa Falasdinawa a Gaza.
Kasashe 142 ciki har da Najeriya ne suka goyin bayan Falasdinawa yayin da Isra'ila da kawayenta tara suka nuna kin amincewa.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun kawo muku jerin kasashen Afrika 4 cikin kasashe 12 da ba su nuna goyon baya ko kin amincewa da kudirin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kasar Kamaru ta yi shiru
Kamaru, wanda ake kira Jamhuriyar Kamaru, ƙasa ce a nahiyar Afirka wacce ke kusa da tarayyar Najeriya.
Kasar tana da yawan jama’a kusan miliyan 28, inda sama da kabilu 250 ke zaune a cikinta, harsunan da 'yan kasar ke aiki da su sun hada da Faransanci, Fulatanci da Turanci.
Tattalin arzikinta ya ta’allaka da noma, mai da katako, amma tana fuskantar ƙalubale kamar talauci sauransu.
Majalisar dinkin duniya ta wallafa cewa Kamaru na cikin kasashen duniya da ba su nuna goyon baya ga Falasdinawa ba ko kuma Isra'ila a kuri'un da aka kada.

Source: AFP
2. Kasar Habasha ma ta yi shiru
Habasha ƙasa ce a gabashin Afirka, kuma tana daga cikin tsofaffin kasashen duniya, kuma kasa ce a Afirka da ba a taɓa yi wa mulkin mallaka ba.
Tana da yawan jama’a sama da miliyan 120, abin da ya sanya ta ta zama ta biyu cikin kasashe mafi yawan jama’a a Afirka.
Addis Ababa ne babban birni, kuma ita ce ke dauke da hedikwatar Tarayyar Afirka kamar yadda kungiyar AU ta wallafa a shafinta.
Kamar kasar Kamaru, ita ma Habasha bata kada kuri'ar goyon bayan Falasdinawa ko nuna adawa da su ba.

Source: Getty Images
3. Kudancin Sudan ta kame baki
Kudancin Sudan da ta samu 'yanci a 2011, ƙasa ce da ba ta da teku a gabashin Afirka wacce ke iyaka da Sudan.
Tana da yawan jama’a kusan miliyan 11, tana fama da rikice-rikicen kabilanci, gudun hijira kuma ɗaya ce daga cikin kasashen da ke fama da manyan rikice-rikicen jin ƙai a duniya.
Tana da al’adu masu yawa tare da fiye da kabilu 60, yaƙin basasa na cigaba da kawo tarnaki ga cigabanta duk da albarkatun ƙasa da take da su.
Duk da cewa babu wani dalili karara da ta bayyana, ita ma bata kada kuri'a ba a makon da ya wuce kamar yadda rahoton Reuters ya nuna.

Source: Getty Images
4. Kongo ta bi sahun Kamaru da Habasha
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ƙasa ce babba a Afirka ta Tsakiya tana cikin kasashe mafi girma a Afirka dangane da fadin ƙasa, mai yawan jama’a fiye da miliyan 100.
Kinshasa ne babban birnin ta kuma tana da yalwar ma’adinai kamar jan karfe da lu’u-lu’u (masu muhimmanci ga fasahar zamani).
Tattalin arzikinta ya dogaro da albarkatun ƙasa, amma BBC ta rahoto cewa ana fama da cin hanci, rikice-rikice a kasar da kuma talauci
Faransanci ne harshen da ake amfani da shi a kasar, amma duk da haka bata goyi bayan Faransa wajen kafa kasar Falasdinawa ba, kamar yadda bata goyi bayan Isra'ila ba.

Kara karanta wannan
Naira ta rike wuta, darajarta ta karu yayin da asusun kudin wajen Najeriya ke habaka

Source: Getty Images
Isra'ila ta yi kisan kare dangi a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa binciken majalisar dinkin duniya ya nuna cewa kasar Isra'ila ta yi kisan kare dangi a Gaza.
Rahoton ya nuna cewa Isra'ila da sojojinta sun aikata manyan laifuffukan da suka shafi hana haihuwa da karfin tsiya a Gaza.
Majalisar dinkin duniya ta bukaci dukkan kasashen duniya su tashi tsaye wajen hana Isra'ila kisan gilla ga Falasdinawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

